Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya amince da kafa wani kwamitin sasanci domin ƙarfafa haɗin kai da daidaito a cikin jam’iyyar APC g...
Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya amince da kafa wani kwamitin sasanci domin ƙarfafa haɗin kai da daidaito a cikin jam’iyyar APC gabanin babban zaɓen da ke tafe.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na jihar, Ahmed Maiyaki, ya fitar, inda ya bayyana cewa an kafa kwamitin ne domin bunƙasa dimokiraɗiyya ta cikin gida, ƙarfafa haɗin kai tsakanin masu ruwa da tsaki, da kuma samar da fahimtar juna tsakanin masu neman takara a faɗin jihar.
Sanarwar ta bayyana cewa kwamitin zai riƙa tattaunawa da masu neman takara, shugabannin jam’iyya da sauran masu ruwa da tsaki domin samar da sulhu a yankunan da ake samun sabanin ra’ayi ko rikicin maslaha tsakanin ‘yan takara.
A cewar Maiyaki, kwamitin zai ƙarfafa masu neman takara da su janye daga takara idan hakan zai taimaka wajen tabbatar da haɗin kai da nasarar jam’iyya a zaɓe mai zuwa.
“Wannan mataki yana nuna ƙudirin Gwamna Uba Sani wajen tabbatar da shugabanci na haɗin kai, zaman lafiya a cikin jam’iyya da kuma kare haɗin kan mambobinta,”
Mataimakiyar gwamnan jihar Hadiza Sabuwa Balarabe ne zata jagoranci kwamitin, yayin da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Yusuf Liman , zai kasance mamba. Sauran mambobin sun haɗa da Shugaban Jam’iyyar APC na Jiha, Sakataren Gwamnatin Jiha (SSG), Shugaban Ma’aikatan fadat Gwamnatin Jihar , Kwamishinan Shari’a kuma Antoni Janar na Jiha, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu, da Mataimakin Shugaban Ma’aikata mai kula da harkokin shari’a, Yayin da Sakataren Jam’iyyar na Jiha ne zai kasance sakataren kwamitin.
Sanarwar ta ƙara da cewa wannan mataki ya yi daidai da manufar Gwamna Uba Sani na ƙarfafa tsarin dimokiraɗiyya ta hanyar tattaunawa, shawara da cimma matsaya cikin lumana domin tabbatar da jam’iyya ta shiga zaɓe cikin haɗin kai da nasara.

No comments