Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Boko Haram Sun Kai Hari Makaranta Tare Da Sace Ɗalibai A Borno

Wasu da ake zargin mayaqan Boko Haram ne sun mamaye wata Makarantar Firamare da Ƙaramar Sakandare da ke ƙauyen Mussa, a Ƙaramar Hukumar Aski...




Wasu da ake zargin mayaqan Boko Haram ne sun mamaye wata Makarantar Firamare da Ƙaramar Sakandare da ke ƙauyen Mussa, a Ƙaramar Hukumar Askira-Uba ta Jihar Borno, inda suka yi awon gaba da adadin ɗaliban da ba a tantance ba.

Majiyoyi daga ƙauyen sun bayyana cewa maharan, waɗanda suka zo da yawa, sun shiga makarantar da ƙarfin tsiya akan babura a ranar Juma’a, jim kaɗan bayan jami’an tsaron sojoji sun bar garin.

Wani mazaunin ƙauyen ya ce an sace yara da dama, sai dai jaridar Daily Trust ba ta sami damar tantance gaskiyar wannan bayani da kanta ba.

“Haka ne, harin ya faru ne da sassafe na yau Juma’a, kuma an gano cewa, an sace yara da dama,” inji wani mazaunin garin.

Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Borno, Hon. Abdullahi Askira ya tabbatar da faruwar harin, sai dai ya ƙi yin sharhi kan ko an sace yara ko a’a.

“Bayanan harin ba su kammala ba tukunna, amma bayanin da nake da shi shi ne cewa ɗalibai da dama sun gudu cikin daji, amma ba ni da cikakken bayani kan waɗanda aka sace,” in ji shi.

Mataimakin Shugaban Majalisar ya bayyana lamarin da cewa, abin takaici ne, inda ya ce maharan sun kai harin ne ’yan mintoci kaɗan bayan dakarun soji da ke sintiri sun bar yankin.

“Wannan yana nuna cewa maharan suna leƙen zirga-zirgar sojojin ne kafin su kawo harin,” in ji shi.

Rubuce-rubuce a kafofin sada zumunta na zamani, musamman a dandalin Facebook, sun yi kira da a taya su da addu’o’i game da harin da kuma zargin sace yaran makarantar.

“Ina kwana, ‘yan uwa masoya. Don Allah mu taya ƙauyen Mussa da addu’a kan harin Boko Haram da aka kai yanzu haka. Kamar yadda rahoton da ke fitowa daga Mussa ya nuna, lamarin ya shafi yaran makaranta,” in ji ɗaya daga cikin masu amfani da dandalin sada zumunta, Solomon Mussa.

No comments