Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Motocin CNG Da Na Lantarki A Kano Don Rage Kuɗin Sufuri

Gwamnatin Tarayya, ta hannun Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Amfani da Iskar Gas (CNG) da Motocin Lantarki (Pi-CNG & EV), ta ƙaddamar da shir...


Gwamnatin Tarayya, ta hannun Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Amfani da Iskar Gas (CNG) da Motocin Lantarki (Pi-CNG & EV), ta ƙaddamar da shirin na shiyyar Arewa a Jihar Kano. Wannan mataki na daga ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na samar da sauƙin sufuri ga al'umma da kuma farfaɗo da tattalin arziki.

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, wanda Mataimakin Babban Jami’in Ma’aikatansa (Deputy Chief of Staff), Ibrahim Hassan Hadeja ya wakilta a gurin taron, ya bayyana cewa sauya ababen hawa zuwa masu amfani da iskar gas da motocin lantarki zai taimaka ƙwarai wajen rage kuɗin sufuri, samar da isasshen makamashi, da kuma tabbatar da ci gaban tattalin arziki mai ɗorewa.

"Kuɗin sufuri yana shafar komai, farashin abinci, masana’antu, zirga-zirgar kayayyaki, da kuma rayuwar talakan Nijeriya. Wannan shiri ba kawai manufar makamashi ba ce; tsari ne na tattalin arziki don bunƙasar ƙasa," in ji Hadeja a madadin Mataimakin Shugaban Ƙasa.

Ya ƙara da cewa an zabi Kano don ƙaddamar da shirin a Arewa ne saboda matsayinta na dabarun kasuwanci, kasancewarta babbar kofa ta kasuwanci tsakanin amfanin shiyyar Arewa da maƙwabtan ƙasashe. Haka kuma, ya yaba wa kamfanoni masu zaman kansu kamar Greenville LNG da NIPCO Gas da suka zuba biliyoyin nairori a fannin gas, sannan ya bayyana zuba jarin Aliko Ɗangote na sayen dubun-dubatar motocin dakon kaya masu amfani da CNG a matsayin abin a yaba. 

A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana ƙaddamar da shirin a matsayin babban alheri da zai rage kuɗin sufuri kai tsaye tare da buɗe ƙofofin habaka tattalin arziki a jihar.

Gwamna Yusuf ya jaddada cewa tuni gwamnatin jihar ta haɗa gwiwa da masu zuba jari don faɗaɗa ayyukan samar da ababen hawa na lantarki da na gas, inda aka ba da filaye ga kamfanonin da ke son kafa rassa a Kano. Ya kuma bayyana cewa shirin zai samar da ayyukan yi ga matasa ta hanyar horar da su fasahar sauya injina zuwa na CNG, gyare-gyare, da harkokin sufuri.

A nasa bangaren, Shugaban Kwamitin Gudanarwa na Shirin, Barr. Ismaeel Ahmed, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba shi umarni na musamman don ya sauya fasalin makamashin gas a Arewacin Nijeriya tare da mayar da Kano babbar cibiyar shirin.

"Shugaban Ƙasa ya shaida mini cewa ba ya son a tuna da shi kawai a matsayin shugaban da ya cire tallafin man fetur, a’a, yana son a tuna da shi a matsayin Shugaban Ƙasa da ya samar da madadin mafita mai ɗorewa ga 'yan Nijeriya," in ji Ahmed.

Ismaeel Ahmed ya bayyana cewa a cikin watanni takwas kacal, shirin ya kafa tashoshin CNG guda biyar da na LNG guda biyu a Kano, sannan an riga an fito da motoci 40 da babura masu kafa uku (daidaita sahu) guda 200. Ya ƙara da cewa ana shirin tura karin motoci 5,000 da manyan motoci guda 200 zuwa Kano nan ba da daɗewa ba.

A gefen taron, Barr. Ismaeel Ahmed ya sanya hannu kan yarjejeniyar fahimta (MoU) da bankin Lotus Bank domin samar da tallafin kudi na biliyoyin nairori don 'yan kasuwa, masu zuba jari, da masu ababen hawa da ke cikin tsarin CNG.



 

No comments