Daga Kwamared Omoniyi M. Akinsiju, PhD Fassara: Aliyu Samba Gabatarwa Muna bin diddigin yadda ’yan hamayya ke ta faman sukar manufofin tatta...
Fassara: Aliyu Samba
Gabatarwa
Muna bin diddigin yadda ’yan hamayya ke ta faman sukar manufofin tattalin arziki na gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda suke ƙoƙarin gurgunta ayyukan da ake yi ta hanyar amfani da kalamai na soki-burutsu ba tare da ƙwararan hujjoji ba.
A mahangar mu, wannan bore da ’yan hamayya ke yi ba shi da wani tushe na ilimi, face dai surutai na son rai da siyasa. Sabanin abin da suke fada, idan aka kalli yanayin tattalin arzikin ƙasar nan tun daga shekarar 2023, za a ga cewa al’amura sun sauya. Ko da yake ba a rasa ƙalubale wajen aiwatar da kowane irin garambawul, mu a gurinmu, manufofin Tinubu sun cimma nasarar farko: wato farfado da bunƙasa fannin masana’antu da kasuwanci (Real Sector) a Najeriya.
Farfaɗowar Ribar Kamfanoni
Wannan farfaɗowa ta shafi yadda kamfanoni masu zaman kansu suka fara samun kuɗaɗen shiga da riba mai tsoka, wanda hakan ke da tasiri ga bunƙasar arzikin kasa (GDP), samar da ayyukan yi, rage raɗaɗin talauci, da kuma samar da dukiya ga jama'a.
Binciken mu ya ginu ne a kan hujjoji na zahiri daga kasuwar hannun jari (NGX) da kuma kananan sana’o’i. Garambawul din da ya jawo girgizar tattalin arziki a farko, yanzu ya fara haifar da da mai ido. Kwanciyar hankali a kasuwar canjin kudi ya sa darajar Naira ta zama ta biyu a karfin daraja a duk faɗin Afirka a cikin wannan shekara.
Nasarorin Manyan Kamfanoni
Mun duba rahoton manyan kamfanoni 20 da ake lissafawa a kasuwar hannun jari, inda suka samu jimillar kuɗin shiga har Naira tiriliyan 27.8 a shekarar 2025. Wannan ya nuna karuwar kashi 28.7 cikin dari idan aka kwatanta da Naira tiriliyan 21.62 da aka samu a 2024.
Ga kadan daga ciki:
• Guinness Nigeria: Ta samu ribar Naira biliyan 41, wanda shi ne karon farko da ta dawo samun riba tun 2023.
• MTN Nigeria: Ta samu ribar tiriliyan 1.7 kafin haraji, bayan da ta yi asarar biliyan 550.3 a shekarar 2024.
• Airtel Africa: Ta samu ribar dala miliyan 328, bayan asarar dala miliyan 89 da ta yi a baya.
• Nigerian Breweries: Kuɗin shigarta ya karu da kashi 68.9 zuwa Naira biliyan 383.6.
• Ɗangote Cement: Ta samu kuɗin shiga na Naira tiriliyan 4.31, karuwar kashi 20.28.
• Seplat Energy: Ta samu tiriliyan 4.14, wanda ya nuna karuwar kashi 150.4.
Ƙananan 'Yan Kasuwa Ma Ba a Bar Su A Baya Ba
Wannan nasara ba ta tsaya ga manyan kamfanoni kadai ba. Rahoton binciken Moniepoint na shekarar 2025 ya nuna cewa ƙananan sana’o’i (Informal Sector) su ma sun samu karuwar kuɗin shiga da kashi 65 cikin dari.
Kammalawa
Wannan gagarumar riba da kamfanoni ke samu ta ba su damar biyan masu hannun jari tiriliyan 1.7 a matsayin rabon riba (payouts). Haka kuma, tana ba da tabbacin ɗorewar ayyukan yi ga ’yan Nijeriya kusan miliyan 9.64 da ke aiki a kamfanoni masu zaman kansu.
A takaice, wannan nasara tana nuna yadda kamfanonin kasar nan suka riga suka saba da sabbin tsare-tsaren gwamnati, kuma suna amfani da basira wajen faɗaɗa ayyukan su da samar da riba mai ɗorewa.

No comments