Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

RIKICIN FILATO: Tinubu Ya Buƙaci Shugabanni Da Masu Ruwa Da Tsaki Su Ajiye Bambancin Domin Samar Da Zaman Lafiya

​A wani mataki na fitar da jihar Filato daga ƙangin tashe-tashen hankula da suka ƙi ci suka ƙi cinyewa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gana da...


​A wani mataki na fitar da jihar Filato daga ƙangin tashe-tashen hankula da suka ƙi ci suka ƙi cinyewa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gana da shugabannin jihar, inda ya ba su umarnin komawa gida su fuskanci juna da zuciya ɗaya domin samar da dawwamamen zaman lafiya.

​Haka zalika, Gwamnatin Tarayya ta amince da sakin kuɗi har Naira Biliyan biyu (N2bn) a matsayin tallafin gaggawa ga mutanen da harin ranar 29 ga watan Maris ya rutsa da su a Unguwar Rukuba da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa.

​Yayin taron wanda aka kwashe sa’o’i uku ana tattaunawa a fadar Shugaban Kasa da ke Abuja ranar Talata, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa lokaci ya yi da shugabanni a kowane mataki za su cire son zuciya, su rungumi juna domin kawo karshen asarar rayuka da dukiyoyi.

​“Ba maganar biki muke yi a nan ba,” in ji Shugaban Kasan. “Muna nan ne domin mu faɗawa juna gaskiya. Idan ana amfani da matasa ana rura wutar gaba da kisan juna, ku shugabanni ya kamata ku fara bincikar kanku.”

​Shugaban ya kuma kalubalanci tawagar, karkashin jagorancin Gwamna Caleb Mutfwang, da su koma su duba duk wasu rahotannin tsofaffin kwamitoci (White Papers) da aka taɓa yi kan rikicin jihar, su fito da hanyoyin da za a bi wajen aiwatar da su.

​Tawagar mai mutum 32 ta haɗa da tsofaffin gwamnonin jihar; Sanata Simon Lalong, Sanata Jonah Jang, Joshua Dariye da Sir Fidelis Tapgun. Sauran sun haɗa da Sarkin Wase, Mai Martaba Mohammed Haruna; Gbong Gwon Jos, Da Jacob Gyang Buba; Shugaban ƙungiyar CAN na jihar, da kuma wakilan matasan Musulmi da Kirista.  

​A nasa ɓangaren, Gwamna Mutfwang ya nuna farin cikinsa, inda ya bayyana cewa wannan ne karon farko da dukkan tsofaffin gwamnonin jihar suka zauna a ɗaki guda domin tattauna makomar jihar. Ya bayyana cewa wannan wata sabuwar baraka ce ta haɗin kai da za ta taimaka wajen dawo da martabar "Gidan Zaman Lafiya da Shaƙatawa."

​Shi ma Mai Martaba Gbong Gwon Jos, Jacob Gyang Buba, ya jinjina wa Shugaban Ƙasan, ya kuma buƙaci a tura ƙarin jami'an tsaro da kuma sanya na'urorin CCTV a lungu da saƙo na birnin Jos. Haka zalika, ya roƙi Shugaban da ya taimaka wajen ganin ’yan gudun hijira (IDPs) sun koma gidajen iyaye da kakanninsu kafin damuna ta kankama.

​Taron ya zo ne a matsayin cika alƙawarin da Shugaba Tinubu ya yi na zama da masu ruwa da tsaki na jihar bayan munanan kashe-kashen da aka yi a watan Maris, inda ya jaddada cewa ba za a zuba ido ana kisan mutane ba tare da an hukunta wadanda ke rura wutar rikicin ba.

​Masana na ganin cewa wannan zama na Abuja zai iya zama silar kawo ƙarshen shekaru da dama na gaba da jidali a jihar, muddin shugabannin suka yi amfani da wannan damar wajen girmama juna da adalci.
 

No comments