Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Tinubu Ya Ƙaddamar Da Cibiyar Farko Ta UNESCO A Duniya Kan Ilimin Kafofin Watsa Labarai Da Bayanai A Abuja

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da Cibiyar Ƙasa da Ƙasa ta Ilimin Kafofin Watsa Labarai da Bayanai (IMILI), wadda ita ce cibiyar farko...

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da Cibiyar Ƙasa da Ƙasa ta Ilimin Kafofin Watsa Labarai da Bayanai (IMILI), wadda ita ce cibiyar farko a duniya ta UNESCO Category 2 da aka ware domin Ilimin Kafofin Watsa Labarai da Bayanai.

An ƙaddamar cibiyar ne a wani gagarumin biki da aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja ranar Laraba.

Shugaba Tinubu, wanda Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Sanata George Akume ya wakilta, ya ce wannan taro wani babban mataki ne ga Nijeriya, Afrika da ma duniya baki ɗaya a ƙoƙarin yaƙi da yaɗa bayanan ƙarya da ruɗarwa, tare da inganta sadarwa mai dacewa a wannan zamani na samun bayanai cikin sauƙi fiye da kowane lokaci.

Ya ce: “Wannan lokaci ne mai tarihi, ba ga Nijeriya da Afrika kaɗai ba, har ma ga al’ummar duniya baki ɗaya. 

"A yau, mun buɗe cibiyar farko ta UNESCO Category 2 kan Ilimin Kafofin Watsa Labarai da Bayanai a ko’ina cikin duniya, a daidai lokacin da buƙatar ta ta fi kowane lokaci girma.”

Yayin da ya waiwaya kan yadda aka kafa cibiyar, Shugaban ya bayyana jajircewar Nijeriya tun bayan karɓar baƙuncin Makon Duniya na 10 kan Ilimin Kafofin Watsa Labarai da Bayanai da aka yi a 2022, da kuma cika alƙawarin kafa IMILI. 

Ya yaba wa ƙoƙarin jami’an gwamnati, da Jakadar Nijeriya a UNESCO, da kuma amincewar baki ɗaya daga ƙasashe membobi 194 na UNESCO a Taron Ƙoli na 43 da aka yi a Samarƙandi.

Shugaba ya jaddada buƙatar gaggawa ta Ilimin Kafofin Watsa Labarai da Bayanai (MIL) a matsayin muhimmiyar hanya ta amfani da bayanai cikin mutunci, yana faɗin: “Bayanan ƙarya na yaɗuwa cikin sauri. Ana amfani da ruɗarwa wajen rarraba al’umma da raunana hukumomi. Kalaman ƙiyayya na rura wutar rikici. Bambanci tsakanin gaskiya da ƙarya na ƙara dusashewa, sau da yawa da gangan. 

"Waɗannan ƙalubale ne na duniya da ke shafar kowace al’umma. Wannan ne ya sa IMILI ba zaɓin da za a iya watsi da shi ba ne; wajibi ne.”

Ya bayyana irin goyon bayan da Gwamnatin Tarayya ke bai wa IMILI, ciki har da samar da kuɗi, tallafin hukumomi ta Buɗaɗɗiyar Jami’ar Nijeriya (NOUN), da haɗin gwiwa da UNESCO kan dokoki da tsarin gudanarwa.

Tinubu ya sake jaddada jagorancin Nijeriya tare da yin kira ga ‘yan kasa baki ɗaya, musamman matasa, da su rungumi ilimin kafofin watsa labarai a matsayin ginshiƙin cigaban ƙasa da na duniya.

“Bari wannan cibiya ta zama fitilar gaskiya, tunani mai zurfi, da sadarwa mai alhaki,” inji shi. 

Ya ƙara da cewa: “Cikin girmamawa nake ayyana Cibiyar Kasa da Kasa ta Ilimin Kafofin Watsa Labarai da Bayanai (IMILI) a hukumance an ƙaddamar da ita.”

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji, Mohammed Idris, a jawabin maraba da baƙi, ya bayyana muhimmancin wannan rana, yana mai cewa IMILI shaida ce ta shirye-shiryen Nijeriya na jagorantar bunƙasa wayayyun ‘yan ƙasa da kare sahihancin bayanai.

Ya yaba da gudunmawar manyan abokan hulɗa, ma’aikata da haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa, tare da sake tabbatar da ƙudirin gwamnati wajen tabbatar da ‘yancin IMILI, ɗorewar ta, da ƙwarewar ta a matakin duniya.

Idris ya ce: “Kafa IMILI ya sanya Nijeriya a sahun gaba a ƙoƙarin da duniya take yi na gina tsayayyun tsarin ilimi, bunƙasa fahimta mai zurfi game da duniyar dijital, da ƙarfafa ‘yancin faɗin albarkacin baki da samun bayanai. 

"IMILI za ta zama cibiyar duniya ta bincike, horarwa da tattaunawar manufofi, tana maraba da malamai, ‘yan jarida, masu tsara manufofi da matasa shugabanni daga ko’ina cikin duniya.”

Manyan baƙi da suka halarci taron sun haɗa da Ƙaramar Ministar Ilimi, Farfesa Suwaiba Sa’id Ahmed; Babbar Sakatariya ta Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Dakta Binyerem Ukaire; Wakiliyar Dindindin ta Nijeriya a UNESCO, Dakta Hajo Sani; Mataimakin Shugaban Jami’ar NOUN, Farfesa Uduma O. Uduma; Wakiliyar UNDP a Nijeriya, Elsie Atafuah; Mataimakiyar Darakta Janar ta UNESCO mai kula da Sadarwa da Bayanai, Ms. Mariya Gabriel; Daraktar IMILI Nijeriya, Dakta Sharon Omotoso; Shugaban NIPR, Dakta Ike Neliaku, tare da sauran su.
 

No comments