Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Rabiu Abdullahi Umar Ya Zama Sabon Shugaban Hukumar NMDPRA

​Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Rabiu Abdullahi Umar a matsayin sabon Shugaban Hukumar Kula da Sashen Man Fetur na Tsaki...

​Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Rabiu Abdullahi Umar a matsayin sabon Shugaban Hukumar Kula da Sashen Man Fetur na Tsakiya da na Kasa (NMDPRA) bayan dakatar da Saidu Mohammed daga muƙamin.

​Wata sanarwa da ta fito daga hannun Bayo Onanuga, Mai Magana da Yawun Shugaban Ƙasa kan fannin Sadarwa da Dabaru a ranar Laraba, ta bayyana cewa wannan mataki ya biyo bayan kare muradun jama'a ne da kuma ƙarfafa ayyukan hukumar.

​Rabiu Abdullahi Umar, wanda naɗin sa ke buƙatar amincewar Majalisar Dattawa, gogge ne kuma ƙwararre ne mai ƙwarewar aiki da ta haura shekara 25 a bangarorin makamashi, masana'antu, da samar da ababen more rayuwa.

​Haka kuma sabon shugaban ƙwararre ne a fannin jagoranci da canza fasalin gudanar da ayyuka a manyan hukumomi. Haka kuma tsohon ɗalibin Jami'ar Bayero ta Kano (BUK) ne a fannin Akanta, ya kuma halarci shahararriyar makarantar kasuwanci ta Jami'ar Harvard (Harvard Business School).

​Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa wannan sauyi ya yi daidai da tanadin Dokar Masana'antar Man Fetur (PIA) ta shekarar 2021. Manufar ita ce inganta tsarin rarraba mai da tabbatar da nasarar tsarin nan na 'Renewed Hope' wajen farfado da tattalin arziki da samar da makamashi.

​A halin yanzu, yayin da ake jiran tantancewar majalisa, babban jami'i mafi daraja a hukumar ta NMDPRA ne zai jagoranci ayyukan hukumar a matsayin mai rikon ƙwarya.

​Daga ƙarshe, Shugaba Tinubu ya gode wa tsohon shugaban hukumar, Saidu Mohammed, kan gudunmawar da ya bayar a lokacin da yake kan karagar mulki, tare da yi masa fatan alheri a ayyukan sa na gaba.
 

No comments