Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Lauyan Jam'iyyar APC Ya Rikiɗe Zuwa Takarar Sanatan Nasarawa Ta Kudu

Daga Zubairu Lawal, Lafia Barista Usman Elegu, tsohon mai ba jam’iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC) shawara kan harkokin shar...


Daga Zubairu Lawal, Lafia

Barista Usman Elegu, tsohon mai ba jam’iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC) shawara kan harkokin shari’a a Jihar Nasarawa ya rikiɗe zuwa takarar kujerar Sanata domin wakiltar Kudancin jihar Nasarawa, tare da alƙawarin aiwatar da ayyukan da za su amfani jama’a idan aka ba shi dama.

Barista Elegu ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan ya sanar da shugabannin jam’iyyar aniyar sa a sakatariyar jam’iyyar da ke Lafia, babban birnin jihar.

Ya ce siyasa tana nufin abin da mutum zai iya bayarwa ga al’umma, yana mai ƙara da cewa yana da duk abin da ake buƙata don yi wa jama’a hidima idan aka ba shi dama.

“Shawarar da na yanke na shiga wannan takara ta samo asali ne daga manufar jin ƙai da kuma kishin jama’a. 

"Idan aka duba halin da ake ciki a yau, manufar mu ita ce sauya yadda siyasa ke gudana. Idan aka ba mu damar yi wa jama’a hidima, za mu sauya tsarin siyasar da ake yi a yau,” in ji shi.

A cewar sa, ƙwarewar sa a siyasa da shugabanci ta fi ta yawancin abokan takararsa, yana mai cewa tarihin aikinsa da gudummawar da ya bayar ga jama’a da jam’iyya a bayyane suke.

“Domin duk waɗanda kuke gani sun zo sun same mu a cikin wannan jam’iyya. Mu ne muka kafa tubalin wannan jam’iyya. Ni kuma na fara siyasa tun kafin su, kuma kun san cewa na san yadda harkokin siyasa ke tafiya.”

“Ba sabon shiga ba ne a jam’iyyar, a matakin jiha, ƙaramar hukuma, gunduma da kuma na ƙasa baki ɗaya. Babu ɗaya daga cikin waɗanda kuka ambata da ke da irin wannan ƙwarewa.

Sai dai ya buƙaci a ba Gwamna Abdullahi Sule goyon baya tare da girmama zabinsa a matsayin shugaban jam’iyyar, yana mai cewa zai tabbatar da cewa duk masu neman takara sun samu dama iri ɗaya kafin zaɓen fidda gwani.

“Ya kamata ku sani cewa ya riga ya faɗi cewa za a gudanar da zaɓe cikin adalci da gaskiya, kuma za mu riƙe shi a kan maganarsa. 

Hakan zai kasance gaskiya da adalci. Ya saba yin hakan kuma zai ci gaba da yi,” in ji shi.
 

No comments