Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya ƙara himma wajen wayar da kan matasa ɗalibai game da ilimin dabarun sarrafa kuɗi tun suna ƙanana, inda ya b...
Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya ƙara himma wajen wayar da kan matasa ɗalibai game da ilimin dabarun sarrafa kuɗi tun suna ƙanana, inda ya buƙaci ɗaliban makarantar sakandare su ɗauki koyon yadda ake sarrafa kuɗi a matsayin muhimmiyar ƙwarewar rayuwa a wannan zamani na sauye-sauyen tattalin arziki.
Wannan jan hankali ya zo ne daga bakin A'isha Isah Olatinwo, yayin da take jawabi a Abuja, wurin bikin Makon Kuɗi na Duniya na shekarar 2026.
Aisha Olatinwo wadda ita ce Daraktar Sashen Kare Masu Amfani da Harkokin Kuɗi da Haɓɓaka Shigar Jama’a Cikin Hadahahar Kuɗi ta CBN, ta jaddada cewa fahimtar yadda kuɗi ke aiki ba zaɓi ba ne ga matasan Nijeriya, wajibi ne.
Ta ce, “A wannan zamani da harkokin kuɗi ke saurin sauyawa, ilimin kuɗi ba wani abu ne na zaɓi ba; abu ne mai matuƙar muhimmanci.” Ta bayyana cewa ikon yanke shawara mai kyau game da kuɗi yana da muhimmanci wajen ci gaban mutum, zaman lafiyar iyali, da bunƙasar tattalin arzikin ƙasa.
Olatinwo ta jaddada cewa koya wa matasa ilimin harkokin kuɗi tun suna ƙanana zai ba su damar fuskantar ƙalubalen tattalin arziki cikin hikima.
Ta ƙara da cewa tattaunawa a fili game da kuɗi na taimakawa wajen kawar da kuskure da gina ƙarfin guiwa.
Daraktar ta CBN ta ce, “Lokacin da muke magana game da kuɗi, muna rushe ra’ayoyi marasa kyau, muna gina ƙarfin guiwa, kuma muna shirya kan mu domin samun makoma mai tsaro ta fuskar kuɗi.”
Ta cigaba da bayyana wasu shirye-shiryen da CBN ya ƙaddamar domin ƙara wayar da kan ‘yan Nijeriya, musamman matasa, kan harkokin kuɗi.
Waɗannan shirye-shiryen sun haɗa da Shirin Wayar da Kan Jama'a Kan Harkokin Banki, wato BECS da kuma manhajar koyon ilimin kuɗi ta “Sabi Money”, waɗanda aka tsara domin koyar da dabarun sarrafa kuɗi tare da ƙarfafa juna tsakanin matasa.
A cewar Olatinwo, shirye-shiryen da aka tanada na wannan shekara an tsara su ne domin koyar da matasa yadda za su riƙa amfani da kuɗi cikin hikima.
Ta ƙara da cewa wayar da kan jama’a ba zai tsaya ga ɗalibai kaɗai ba, har ma zai haɗa da iyaye, ‘yan kasuwa, da al’ummomin karkara a faɗin ƙasa.
Olatinwo ta bukaci mahalarta taron su sake tunanin yadda suke kallon kuɗi, tana ƙarfafa su da cewa su daina kallon kuɗi a matsayin abin kashewa kawai, su ɗauke shi a matsayin hanyar saka jari.
Ta ce, “Kada mu ga kuɗi a matsayin abin kashewa kawai. Ku yi wa kuɗi kallo a matsayin kayan saka jari. Idan kuka saka jari, ribar da za a samu daga baya za a iya kashewa. Haka ake gina arziki.”
Tun da farko, Shugaban Sashen Ilimantar da Masu Amfani da Kimanta Shirye-shirye na CBN, Amuwa Nelson, ya bayyana Makon Kuɗi na Duniya a matsayin wani shiri na duniya da aka ƙirƙira domin bai wa matasa ilimi, ƙwarewa, da ƙarfin guiwar yanke shawarar kuɗi cikin hikima.
Ya bayyana cewa an tsara bikin ilimin kuɗi na wannan shekara domin bai wa mahalarta damar koyon yadda ake tsara kasafin kuɗi, ajiyar kuɗi, da kashe kuɗi cikin hikima, tare da nuna musu damar kuɗi da suke da ita.
Da yake magana kan taken bana, “Smart Money Talks”, Nelson ya ce taken yana ƙarfafa tattaunawa a fili game da kuɗi a matsayin hanyar yanke shawara mai kyau.
Ya ce yin tambayoyi, musayar ra’ayoyi, da koyo daga wasu muhimman matakai ne wajen gina makoma mai tsaro ta fuskar kuɗi.
Ya ƙara da cewa mahalarta za su samu damar tattaunawa kai tsaye da cibiyoyin kuɗi, gano kayayyakin kuɗi da aka tsara domin matasa, da kuma samun ilimin da zai taimaka musu wajen yanke shawara mai kyau a yanzu da kuma nan gaba.

No comments