Daga Zubairu Lawal, Lafia Tawagar APC magoya bayan tsohon Sufeto Janar na ‘yan sanda, Mohammed Abubakar Adamu, ta yi watsi da Ɗan Takarar Gw...
Tawagar APC magoya bayan tsohon Sufeto Janar na ‘yan sanda, Mohammed Abubakar Adamu, ta yi watsi da Ɗan Takarar Gwamna da Gwamna Abdullahi Sule ya tsayar a Jihar Nasarawa.
Magoya bayan jam'iyyar sun bayyana wannan mataki a matsayin wanda ya saɓa wa kundin tsarin mulki, kuma barazana ga dimokuraɗiyyar cikin gida a jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Tawagar ta bayyana wannan matsayi ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a Cibiyar ‘Yan Jarida ta NUJ da ke Lafia, inda Darakta Janar na Ƙungiyar Yaƙin Neman Zaben Mohammed Abubakar Adamu a matsayin Gwamnan jihar Nasarawa a 2027.
Hon. Barr. Musa Hussein, ya yi wa ‘yan jarida bayani kan sabbin sauye-sauyen siyasa a jihar.
Hussein ya soki rahotannin da ke danganta Gwamna Abdullahi Sule da ɗaukar wani ɗan takara kafin gudanar da zaɓen fidda gwani na jam’iyya, yana mai jaddada cewa irin waɗannan matakai sun saɓa wa kundin tsarin mulkin APC.
A cewar sa, kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanadi hanyoyi guda biyu kacal na halal da za a bi domin fitar da ɗan takara, wato zaɓen fidda gwani kai tsaye (direct primaries) ko kuma yarjejeniya (consensus).
yana gargadin cewa duk wani yunƙuri na ƙaƙaba ɗan takara ba tare da bin waɗannan hanyoyi ba ba shi da ingancin doka.
Ta kuma fayyace cewa babu wani sahin zance daga shugabancin jam’iyyar ta ƙasa da ya sanya baki kan wanda ya cancanta da Takarar Gwamna a Jihar Nasarawa.
Haka zalika tawagar magoya bayan Adamu Sun zargi Gwamnati da tilasta wa masu riƙe da muƙaman Gwamnati masamman Shugabannin Ƙananan Hukumomi da Kansiloli da su goyi bayan Dan Takarar.

No comments