Gwamnatin Tarayya ta jinjina wa Masarautar Saudiyya bisa samar da guraben karatu na kyauta ga ɗaliban Nijeriya su 50 domin karantar fannin m...
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al'umma, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan yayin da ya karbi baƙuncin Jakadan Saudiyya a Nijeriya, Yousef Bin Mohammed Al-Balawi, wanda ya ziyarce shi a ofishin sa da ke Abuja ranar Litinin, 27 ga watan Afrilu, 2026.
Ministan ya bayyana cewa wannan tallafin karatu ya zo daidai da burin gwamnati na bunƙasa ilimi da ƙwarewa a fannonin da suka shafi tattalin arzikin ƙasa. Ya ce wannan ba gurbin karatu ba ne kawai, a’a, wani babban jari ne da za a zuba wa matasan Nijeriya.
"Wannan mataki zai samar da ƙwararrun da Nijeriya ke buƙata a masana’antun man fetur da ma’adanan ƙasa," in ji Ministan.
Ya kuma ƙara da cewa an tsara shirin ta yadda ɗalibai 50 za su riƙa amfana a duk shekara, wanda hakan zai tabbatar da ɗorewar shirin na dogon lokaci.
A nasa bangaren, Jakada Al-Balawi ya sanar da cewa gurbin karatun ya fito ne daga Jami’ar Man Fetur da Ma’adanai ta King Fahd (KFUPM). Ya bayyana cewa tallafin ya haɗa da Biyan kuɗin makaranta (Tuition), Tikitin jirgin sama na zuwa da dawowa, Wajen kwana kyauta, da Alawus ɗin da ke shiga hannu a kowane wata.
Jakadan ya jaddada cewa wannan ƙoƙari na nuna kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu. Yana mai cewa Saudiyya da Nijeriya ginshiƙan tattalin arziki ne a yankunan su waɗanda ke da damar bunƙasa hulɗar kasuwanci a tsakanin su.
Ministan ya kuma yi amfani da damar wajen bayyana jimamin Nijeriya game da taƙaddamar da ke faruwa a yankin tekun Gulf, inda ya miƙa saƙon goyon bayan Nijeriya ga ƙasar Saudiyya. Ya bayyana fatan samun zaman lafiya da kuma daidaita duk wata matsala ta hanyar diflomasiyya.
A ƙarshen zaman, Ministan ya tabbatar wa Jakadan cewa Nijeriya za ta gaggauta aiwatar da sauran yarjeneniyoyin da aka ƙulla da Saudiyya, ciki har da waɗanda suka shafi fannin yaɗa labarai da sauran sassa.
Ziyarar ta samu halartar Babban Sakataren ma'aikatar, Dr. Binyerem C. Ukaire, da wasu manyan daraktoci na ma'aikatar yaɗa labaran.

No comments