Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

DALLA-DALLA: Yadda CBN Ya Bankaɗo 'yan Damfara Ta Intanet, Masu Ƙoƙarin Kutsen Satar Kuɗaɗen Ajiyar Kwastomomin Bankuna

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya fitar da sabon gargaɗi kan masu ƙoƙarin damfara ta Intanet, inda  a ranar 22 ga Afrilu, 2026, aka wayi gari ...



Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya fitar da sabon gargaɗi kan masu ƙoƙarin damfara ta Intanet, inda 
a ranar 22 ga Afrilu, 2026, aka wayi gari da sanar da jama’a game da ƙaruwar saƙonnin bogi ta imel, saƙonnin waya, da damfara ta yanar gizo da ake yi da sunan CBN.


Hanyoyi 5 Da 'Yan Damfara Ke Amfani Da Su:

Kwaikwayon CBN:

Masu damfara suna yaɗa saƙonni da bayanai na bogi ta yanar gizo, suna iƙirarin cewa sun fito daga CBN domin satar bayanan sirri da na kuɗi na mutane.

'Links' Masu Cutarwa:

Saƙonnin suna ƙarfafa mutane su danna hanyoyin shiga manhajoji (links) waɗanda ke kaiwa zuwa shafukan damfara domin kutsawa cikin asusun banki.


Yaɗa Ƙarya:

Masu damfara suna yaɗa bayanan ƙarya game da shugabancin bankin, bayar da lasisi, da manufofin CBN domin samun amincewar jama’a.


Gargaɗin CBN Ga Jama’a:

A Yi Amfani da Shafin Ainihi na CBN Kawai:

CBN ya sake jaddada cewa shafin yanar gizon hukuma guda ɗaya kacal shi ne www.cbn.gov.ng⁠�.


Kare Bayanan ka na Sirri:

Kada ka taɓa bayar da bayanan sirri, bayanan shiga asusun banki, ko lambar BVN ta imel, kafofin sada zumunta, ko kira daga wanda ba ka sani ba.

Tabbatar Kafin Ka Danna 'Link':

Ka guji danna 'links' da ka ke shakku ko shiga shafukan da ba a tabbatar da sahihancin su ba, ko da sun yi kama da na CBN.

Kai Rahoton Damfara:

Duk wani saƙo, imel, ko shafin damfara da ake zargi ya kamata a kai rahoto ga jami’an tsaro ko reshen CBN mafi kusa.

Matakan Da CBN Ke Ɗauka:

Wannan gargaɗi ya biyo bayan hare-haren yanar gizo da aka kai wa wasu hukumomin gwamnati kamar Hukumar  Rajistar Kamfanoni, wato Corporate Affairs Commission (CAC).

A matsayin martani, CBN ta:
Umurci bankuna da su kammala cikakken binciken tsaron yanar gizo cikin makonni uku daga watan Afrilu 2026.

Ƙaddamar da sabbin ƙa’idojin Bank Verification Number (BVN) waɗanda za su fara aiki daga 1 ga Mayu, 2026, domin rage damfara.

Ƙayyade amfani da manhajar banki ta waya zuwa na’ura guda ɗaya kacal domin ƙara tsaro.
 

No comments