Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya yi gargaɗi kan yawaitar saƙonnin zamba da suka ƙunshi imel sauran hanyoyin sadarwa ta yanar gizo na bogi, i...
A cikin wata sanarwa da aka fitar a daren Talata, wanda A Daraktar Sadarwa ta CBN, Hakama Sidi Ali ta sanya wa hannu, CBN ya bayyana cewa waɗannan saƙonnin bogi suna ɗauke da ƙarairayi game da shugabancin bankin, bayar da lasisi, da manufofin sa.
Sanarwar ta ce masu aikata wannan damfara suna amfani da bayanan yaudara domin jan hankalin mutane su danna hanyoyin shiga manhajoji (links) masu haɗari, wanda zai iya ba su damar shiga asusun ajiyar kuɗin mutum, ba tare da izini ba.
Sanarwar ta ce:
“CBN na sanar da jama’a cewa ana yaɗa saƙonnin bogi, imel, da hanyoyin sadarwa ta yanar gizo waɗanda ake ƙoƙarin nuna cewa sun fito daga CBN ko suna da alaƙa da shi, domin yaudarar jama’a.
Waɗannan saƙonnin bogi suna ƙarfafa masu karɓa su danna hanyar shiga wata manhaja, suna yaɗa ƙarya game da shugabancin bankin, bayar da lasisi, da manufofi, kuma manufar su ita ce kutse cikin asusun ajiyar kuɗaɗen jama'a.”
CBN ya jaddada cewa shafin yanar gizon hukuma na bankin shi ne www.cbn.gov.ng.
Yana gargaɗin jama’a da kada su danna links ko su bayar da bayanan su na sirri a shafukan da ake zargi.
Bankin ya kuma shawarci jama’a da su tabbatar da sahihancin duk wata sanarwa daga CBN ta hanyar duba shafin yanar gizon hukuma ko kuma kafofin watsa labarai da aka amince da su.
Haka kuma, CBN ya buƙaci jama’a su kai rahoton duk wani shafi, imel, ko saƙon bogi ga hukumomin tsaro.
Babban bankin ya sake jaddada ƙudurin sa na kare tsarin kuɗi na Nijeriya tare da ƙarfafa matakan tsaron yanar gizo, tare da haɗin gwiwa da hukumomin da suka dace domin kare jama’a daga damfara ta hanyoyin sadarwar zamani, wato dijital.

No comments