Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Oluremi Tinubu Ta Ƙaddamar Da Shirin ECoN A Kano, Ta Buƙaci Mayar Da Hankali Kan Masana’antu

Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta ƙaddamar da wani sabon shiri mai taken “Energise Commercialisation Now” (ECoN) a birnin K...


Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta ƙaddamar da wani sabon shiri mai taken “Energise Commercialisation Now” (ECoN) a birnin Kano ranar Alhamis, inda ta yi kira ga ‘yan Nijeriya da su daina tsayawa ga tunanin ayyuka kawai, maimakon haka su duƙufa wajen gina masana’antu.

Da take jawabi a wajen taron, Sanata Oluremi ta bayyana cewa Nijeriya ƙasa ce mai cike da fasaha da hazaka, inda kullum ake samun sabbin ra’ayoyi daga jami’oi da cibiyoyin fasaha, amma abin takaicin shi ne yawancin waɗannan ra’ayoyin ba sa komawa ayyukan da za su amfani al’umma a aikace.

Manufar shirin ECoN

Uwargidan Shugaban Ƙasar ta ce: “Wannan shiri na ECoN wani gagarumin mataki ne na dinke barakar da ke tsakanin tunanin ayyuka da aiwatar da su. Muna son samar da yanayi inda za a tallafa wa ra’ayoyin matasa da masu bincike domin su zama manyan masana’antu.”

Ta ƙara da cewa shirin zai taimaka kwarai wajen samar da ayyukan yi, bunƙasa tattalin arziki, da kuma sanya Nijeriya takara da sauran ƙasashen duniya a fagen kasuwanci da fasaha. Ta kuma nanata cewa mata da matasa ne za su kasance a gaba-gaba a dukkan shirye-shiryen gwamnati.

A nasa jawabin, Ministan Fasaha da Kimiyya, Dr. Kingsley Udeh, ya ce an samar da ECoN ne domin magance tsohuwar matsalar nan ta Nijeriya, inda ake bincike mai kyau amma ba a kai shi kasuwa domin ya zama kuɗi.

A cewarsa, bincike da dama na nan sun maƙale a dakunan gwaje-gwaje (laboratories) saboda rashin kuɗi ko kuma rashin hanyar kai su ga masu saye.

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nuna jin daɗinsa kan yadda aka zaɓi Kano domin ƙaddamar da wannan shiri na ƙasa da kuma na shiyyar Arewa maso Yamma. Ya bayyana cewa Kano ta riga ta fara shiri ta hanyar inganta ilimin kimiyya da fasaha da kuma faɗaɗa hanyoyin sadarwa na zamani (ICT).

Shi ma Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, wanda ya yi magana a madadin Gwamnonin Arewa maso Yamma, ya lashi takobin cewa gwamnonin shiyyar za su ba da cikakken haɗin kai. Ya bayyana cewa Jihar Jigawa ma na shirin kafa "Garuruwan Fasaha" (Technology Village) domin bunkasa harkar bincike da jan hankalin masu zuba jari.





 

No comments