Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce babban taron jam’iyyar APC na ƙasa da za a yi zai nuna haɗin kai, ɗa’a, ...
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce babban taron jam’iyyar APC na ƙasa da za a yi zai nuna haɗin kai, ɗa’a, da sadaukarwa ga cigaban Nijeriya.
Idris ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a Abuja a lokacin ƙaddamar da Kwamitin Yaɗa Labarai na Babban Taron APC na shekarar 2026. Ministan shi ne ɗaya daga cikin shugabanni biyu na kwamitin.
Yayin da ya bayyana taron a matsayin “wani babban mataki” ga jam’iyyar mai mulki, Idris ya ce wannan dama ce ta ƙarfafa tsarin dimokiraɗiyya a cikin jam’iyyar da kuma tabbatar da burin APC na ganin Nijeriya ta kasance tsintsiya-maɗaurin-ki-ɗaya kuma mai wadata.
Ya ce: “Babban taron ƙasa da ke tafe zai ba jam’iyyar damar nuna haɗin kai, ɗa’a, da sadaukarwa ga cigaban ƙasa.”
Idris, wanda ya yi jawabi ta kafar intanet daga Birtaniya, ya ce gwamnatin Tinubu tana aiwatar da manyan gyare-gyare domin sake sanya Nijeriya kan tafarkin cigaba mai ɗorewa.
Ya ƙara da cewa APC za ta ci gaba da tallafa wa Shirin Sabunta Fata na Shugaban Ƙasa.
Haka kuma, ya jaddada muhimmancin aikin Kwamitin Yaɗa Labarai wajen tabbatar da nasarar taron.
“Aikin da aka ɗora wa wannan kwamitin yana da matuƙar muhimmanci. Nasarar kowane babban taron siyasa ya dogara ne matuƙa kan yadda aka isar da saƙon sa ga jama’a yadda ya kamata,” inji shi.
Ya ƙara da cewa, “Ta hanyar amfani da duk kafafen watsa labarai da muke da su, dole ne mu tabbatar da cewa an yaɗa taron sosai da kyau, tare da kiyaye inganci da gaskiya.”
A ƙarshe, Ministan ya ƙaddamar da kwamitin, ya taya membobin murna, sannan ya yi masu fatan samun nasara a ayyukan su.
An shirya gudanar da babban taron daga ranar 25 zuwa 28 ga watan Maris, 2026.

No comments