Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

KARRAMAWAR WINDSOR CASTLE: Tinubu Ya Kafa Tarihi Na Zama Zababben Shugaban Nijeriya Na Farko Da Aka Karrama

  Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya nufi birnin London na kasar Burtaniya domin gudanar da wata gagarumar ziyarar ban-girma (State Visit), ...

 



Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya nufi birnin London na kasar Burtaniya domin gudanar da wata gagarumar ziyarar ban-girma (State Visit), wadda ita ce irinta ta farko da wani shugaban Najeriya ya kai kasar cikin shekara 37.

Sarki Charles III da matarsa Sarauniya Camilla ne suka gayyaci Shugaba Tinubu, inda za su karbe shi da uwargidansa, Sanata Oluremi Tinubu, a gidan sarauta na Windsor Castle daga ranar Laraba zuwa Alhamis.

Wannan ziyara ta kafa tarihi ta fuskoki da dama:
1. Shekara 37: Rabon da wani shugaban Najeriya ya kai ziyarar aiki irin wannan tun a shekarar 1989, lokacin mulkin Janar Ibrahim Badamasi Babangida.

2. Windsor Castle: Tinubu ne shugaban Najeriya na farko da Sarkin Burtaniya zai karba a wannan katafaren gidan sarauta na Windsor; dukkan shugabannin baya a Buckingham Palace aka karbe su.

3. Mulkin Dimokuradiyya: Wannan ne karon farko da Burtaniya ta karrama zababben shugaban Najeriya tun bayan komawar kasar tafarkin dimokuradiyya a shekarar 1999.

Baya ga bukukuwan karramawa da za a yi wa shugaban, akwai manyan batutuwan da za su tattauna, musamman kan tattalin arziki:
• Yarjejeniyar Jiragen Ruwa: Ana sa ran sanya hannu kan wata yarjejeniyar kudi har fam miliyan £746 (kimanin dala biliyan daya) domin gyara manyan tashoshin jiragen ruwan Najeriya na Apapa da Tin Can dake Legas.
• Hulɗar Kasuwanci: Shugaba Tinubu zai gana da Firayim Minista Keir Starmer a fadar 10 Downing Street domin tattauna batun kasuwanci, tsaro, da kuma batun biza (immigration).
• Zuba Jari: Shugaban zai gabatar da manufofinsa na gyaran tattalin arziki ga ’yan kasuwar Burtaniya domin jawo su su zuba jari a fannonin hakar ma’adinai, makamashi, da kere-kere a Najeriya.

A ranar Laraba, shirin zai hada da hawan keken doki na alfarma zuwa Windsor Castle, buga taken kasashen biyu, da kuma harba bindigogi 21 don girmama shugaban. Haka kuma, za a yi gagarumar liyafar cin abincin dare (State Banquet) a gidan sarautar domin girmama daukacin tawagar shugaban.

Wannan ziyara wata dama ce ta sabunta dangantakar dake tsakanin Najeriya da tsohuwar uwar gidanta, musamman ganin yadda kasashen biyu ke neman sabbin abokan hulda a daidai lokacin da tattalin arzikin duniya ke fuskantar kalubale.
 

No comments