Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna alhininsa game da sabon harin ta’addanci da aka kai birnin Maiduguri na Jihar Borno, inda ya bayyana...
Cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 17 ga watan Maris, 2026, Shugaba Tinubu ya jajanta wa mutanen da suka rasa rayukan su da kuma waɗanda suka jikkata, yana mai jaddada cewa gwamnati na tare da jama’ar Jihar Borno a wannan mawuyacin lokaci.
Shugaban ya bayyana cewa waɗannan hare-hare na nuna alamun fargaba da matsin lamba da ’yan ta’addan ke fuskanta daga dakarun tsaron Najeriya.
> "Waɗannan ayyukan ta’addanci yunƙuri ne na ƙarshe na matsananciyar fargaba da waɗannan masu laifin ke yi domin dasa tsoro a zukatan mutane, sakamakon irin luguden wutar da suke fuskanta daga jami’anmu." Inji Tinubu
Tinubu ya ƙara da cewa, a taron tsaro da ya gudanar a ƙarshen makon jiya, ya amince da samar da ƙarin kayan aiki da tallafin ayyuka ga hukumomin tsaro domin ƙarfafa dabarunsu na yaƙi da ta’addanci.
Domin tabbatar da an magance lamarin cikin gaggawa, Shugaba Tinubu ya ba wa manyan hafsoshin tsaro na ƙasa umarnin gaggawa na su koma birnin Maiduguri domin jagorantar ayyukan tsaro da kansu.
Haka kuma, ya umarci hukumomin agajin gaggawa da su tabbatar da sun ba wa duk waɗanda suka jikkata kulawar da ta dace.
A ƙarshe, Shugaban ya jaddada cewa babu wani lungu a Najeriya da zai zama wurin buya ga ’yan ta’adda, inda ya ce: "Ba za mu taba mika wuya ga tsoro ba. Za mu nemo su, mu fuskance su, kuma mu murƙushe su baki ɗaya."

No comments