Fadar Shugaban Ƙasa ta sanar da cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Lamido Abubakar Yuguda a matsayin Mataimakin Gwamnan Babba...

Fadar Shugaban Ƙasa ta sanar da cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Lamido Abubakar Yuguda a matsayin Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), sai dai naɗin zai fara ne bayan Majalisar Dattawa ta tabbatar da shi.
Sanarwar ta fito ne daga Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai da Tsare-tsare, Bayo Onanuga, a ranar Laraba.
A cewar sanarwar, an yi wannan naɗi ne bisa tanadin Sashe na 8(1) na Dokar Babban Bankin Najeriya ta shekarar 2007.
Naɗin Yuguda ya biyo bayan naɗin tsohon Mataimakin Gwamnan CBN, Bala Bello, a matsayin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Tattalin Arziki da Siyasa.
Shugaba Tinubu ya buƙaci sabbin masu riƙe da mukaman su gudanar da ayyukansu cikin ƙwazo, ƙwarewa da sadaukarwa domin tabbatar da daidaiton tattalin arzikin Najeriya da kuma bunƙasa shi.
Tarihin Lamido Yuguda
Lamido Yuguda ya taɓa riƙe muƙamin Daraktan Janar na Hukumar Kula da Kasuwar Hada-hadar Kuɗi ta Nijeriya (SEC) daga shekarar 2020 zuwa 2024.
Yuguda ya kammala karatunsa a Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) Zariya inda ya samu digirin B.Sc a fannin Accountancy a shekarar 1983. Daga bisani ya samu digiri na biyu (Master’s) a fannin Money, Banking and Finance daga Jami’ar Birmingham da ke Birtaniya a shekarar 1991.
Shi mamba ne na ƙwararrun ‘Institute of Chartered Accountants of Nigeria’ (ICAN) kuma yana da shaidar ƙwararrun masu nazarin jarin kasuwa ta CFA.
Yuguda ya fara aikinsa ne a Babban Bankin Najeriya (CBN) a shekarar 1984 a matsayin Babban Mai Kulawa (Senior Supervisor) a Sashen Ayyukan Kuɗaɗen Ƙasashen Waje.
A shekarar 1997 ya shiga Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) a matsayin masanin tattalin arziki a sashen Afirka, inda ya yi aiki har zuwa 2001 kafin ya koma CBN.
Ya yi ritaya daga CBN a shekarar 2016 bayan ya yi shekaru shida a matsayin Daraktan Sashen Kula da Ajiyar Kuɗaɗen Ƙasa (Reserve Management Department).
No comments