Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Babban Burin Mu Mayar Da Kaduna Cibiyar Noma Da Kiwo A Arewacin Nijeriya — Uba Sani

Gwamnan Jihar Kaduna State, Uba Sani, ya bayyana cewa babban burin gwamnatinsa shi ne mayar da jihar cibiyar noma da kiwo mafi girma a Arewa...

Gwamnan Jihar Kaduna State, Uba Sani, ya bayyana cewa babban burin gwamnatinsa shi ne mayar da jihar cibiyar noma da kiwo mafi girma a Arewacin Nijeriya

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wani shiri da gwamnatinsa ta gudanar na raba tallafi ga ƙungiyoyin manoma kusan 5,000 a sassa daban-daban na jihar domin ƙarfafa harkar noma da kiwo.

Uba Sani ya ce tallafin da aka bayar zai taimaka wajen ƙara yawan amfanin gona, inganta kiwo, da kuma samar da ayyukan yi ga dubban matasa da manoma a karkara. Ya ƙara da cewa matakin wani ɓangare ne na dabarun gwamnatinsa na bunƙasa tattalin arzikin karkara da rage talauci.

A cewarsa, gwamnatinsa za ta ci gaba da zuba jari a fannin noma da kiwo ta hanyar samar da kayan aiki na zamani, horar da manoma, da kuma tallafawa ƙungiyoyin manoma domin su samu damar haɓaka ayyukansu.

Gwamnan ya jaddada cewa idan aka ci gaba da aiwatar da waɗannan tsare-tsare yadda ya kamata, jihar Kaduna za ta zama jagora wajen noma da kiwo a Arewacin ƙasar, tare da taka muhimmiyar rawa wajen samar da abinci da bunƙasa tattalin arzikin Nijeriya.


 

No comments