Gwamnatin Jihar Kaduna ta musanta wani rahoto da ke yawo a kafafen sada zumunta bisa zargin cewa gwamnan jihar, Malam Uba Sani, ya goyi baya...
Gwamnatin Jihar Kaduna ta musanta wani rahoto da ke yawo a kafafen sada zumunta bisa zargin cewa gwamnan jihar, Malam Uba Sani, ya goyi bayan wasu ’yan takara domin kujerun majalisar tarayya gabanin zabukan 2027 masu zuwa.
Gwamnatin ta bayyana rahoton a matsayin mara rushe tare da buƙatar al’umma su yi watsi da shi baki daya.
A wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Ahmed Maiyaki, ya sanya wa hannu , ya ce gwamna Uba Sani bai goyi bayan kowane dan takara ba, kuma bai fifita wani mai neman wata kujera ta zabe ba.
Sanarwar ta bayyana cewa gwamnan mai kishin dimokuradiyya ne, wanda ya yi imani da tsarin gaskiya da adalci, inda ’yan jam’iyya da masu ruwa da tsaki za su zabi ’yan takararsu ta hanyoyin da kundin tsarin jam’iyya ya tanada.
Sanarwa ta ci gaba da cewa " Mun sanu wani sako mai rudani da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa gwamna ya goyi bayan wasu ’yan takara. Wannan ikirari ƙarya ne gaba ɗaya, kuma bai da tushe balle makama,”
Malam Maiyaki , ya ƙara da cewa a halin yanzu gwamnan ya fi maida hankali ne wajen inganta shugabanci nagari da aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da za su kyautata rayuwar al’ummar jihar Kaduna, maimakon shiga batun goyon bayan ’yan takara tun kafin lokaci.
Sanarwar ta kuma gargaɗi mutane ko ƙungiyoyi da su guji yaɗa labaran ƙarya da bayanan siyasa marasa tushe, domin irin hakan na iya haifar da ruɗani a fagen siyasa tare da yaudarar jama’a.
Akan haka Kwamishinan ya buƙaci ’yan siyasa da magoya baya da sauran jama’a da su rika tabbatar da sahihancin labarai daga sahihan majiyoyi kafin yaɗawa, yana mai cewa sadarwa mai kyau na da muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.
Maiyaki ya jaddada cewa gwamna Uba Sani zai ci gaba da mutunta hakkokin dimokuradiyya na dukkan masu neman takara, tare da tabbatar da cewa doka da ka’idoji ne za su jagoranci dukkan harkokin siyasa a jihar.

No comments