Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Tarayya Na Shirin Faɗaɗa Amfani Da Gas Da Motocin Lantarki Don Rage Tsadar Sufuri — PCNGi

Shugaban Hukumar Presidential Compressed Natural Gas Initiative (PCNGi), Ismaeel Ahmad, ya ce gwamnati na ƙara ƙaimi wajen faɗaɗa amfani da ...


Shugaban Hukumar Presidential Compressed Natural Gas Initiative (PCNGi), Ismaeel Ahmad, ya ce gwamnati na ƙara ƙaimi wajen faɗaɗa amfani da gas da motoci masu amfani da lantarki domin rage tsadar sufuri a Najeriya.

Ismaeel ya bayyana haka ne bayan ganawarsa da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, inda suka tattauna kan hauhawar farashin fetur da rikicin Gabas ta Tsakiya ya haddasa, da kuma hanyoyin da shirin PiCNG da motocin lantarki (EV) za su taimaka wajen magance matsalar.

Ya ce ya gabatar wa shugaban ƙasar da shirin da hukumar ke da shi na faɗaɗa cibiyoyin cika gas (refuelling stations) a sassan ƙasar, tare da samar da kayan canza motoci zuwa CNG domin masu ababen hawa da ke son sauyawa daga fetur zuwa gas.

A cewarsa, shirin ya haɗa da tura babura masu ɗaukar fasinjoji uku (keke napep) da kuma kafa cibiyoyin cajin motocin lantarki, domin tallafa wa hanyoyin sufuri masu rahusa ga ’yan Najeriya.

Shugaban na PCNGi ya jaddada cewa manufar shirin ita ce rage kuɗin sufuri ga jama’a, tare da ƙara bunƙasa amfani da gas da lantarki a matsayin hanyoyin makamashi masu araha a harkar zirga-zirga.



 

No comments