Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, tare da mai ɗakin sa, Sanata Oluremi Tinubu, sun isa ƙasar Birtaniya a ranar Talata domin gudanar da gagaru...
Ziyarar dai ta biyo bayan gayyatar da Sarki Charles III da Sarauniya Camilla suka yi wa shugaban na Najeriya.
Jirgin shugaban ƙasar ya sauka ne a filin tashi da saukar jiragen sama na Stansted da ke Landan da misalin karfe 3:18 na yammacin ranar Talata.
Wata sanarwa da ke ɗauke da sa hannun Bayo Onanuga, Mai Magana da Yawun Shugaban kan Harkokin Yaɗa Labarai da Tsare-tsare, ta bayyana cewa Mataimakin Wakilin Masarautar Birtaniya a yankin Essex, Mark Bevan, ne ya tarbi shugaban a madadin gidan sarautar.
Sauran waɗanda suka tarbi shugaban sun haɗa da Muƙaddashin Babban Jakadan Nijeriya a Birtaniya, Ambasada Mohammed Maidugu, da wasu manyan jami’an gwamnati. Haka kuma, wasu gwamnoni da sanatoci da ministoci sun hallara a masaukin shugaban domin yi masa barka da zuwa.
Za a karbi baƙuncin Shugaba Tinubu da matarsa a Fadar Windsor (Windsor Castle) tun daga ranar Laraba 18 ga watan Maris zuwa Alhamis 19 ga watan.
Babban maƙasudin wannan ziyara dai shi ne karfafa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu, tare da lalubo hanyoyin bunƙasa jari ga ‘yan kasuwar Nijeriya da na Birtaniya.






No comments