Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

2027: Gwamnan Anambara Ya Roƙi Igbo Su Mara Wa Tinubu Baya Don Kada Su Bata Ƙuri’un Su

Gwamnan Jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, ya buƙaci al’ummar yankin Kudu-maso-gabas da su mara wa Shugaba Bola Tinubu baya a zaɓen gam...

Gwamnan Jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, ya buƙaci al’ummar yankin Kudu-maso-gabas da su mara wa Shugaba Bola Tinubu baya a zaɓen gama-gari na 2027.

Soludo ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin rantsar da shi karo na biyu, wanda aka gudanar a dandalin Dakta Alex Ekwueme Square da ke Awka, babban birnin Jihar Anambra.

Alƙalin Alƙalan Jihar Anambra, Onochie Anyachebelu, shi ne ya rantsar da Soludo tare da karɓar rantsuwar aiki da ta biyayya da ƙarfe 11:47 na safe.

Haka kuma Anyachebelu ya rantsar da mataimakin gwamnan jihar, Onyekachukwu Ibezim, da ƙarfe 11:52 na safe.

Taron ya samu halartar Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima da tsofaffin shugabannin ƙasa Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan.

Da yake jawabi ga mahalarta taron, Soludo ya ce bai kamata 'yan yankin Kudu-maso-gabas su “ɓata” ƙuri’un su kan wasu ’yan takara ba a zaɓen na shugaban ƙasa da ke tafe, yana mai cewa ya dace su mara wa Tinubu baya.

Soludo ya nuna cewa makomar siyasar Inyamirai tana da matuƙar muhimmanci, amma ya nuna cewa lokacin da yankin zai fitar da shugaban ƙasa bai zo ba.

Gwamnan ya ce yankin yana da ƙwarin gwiwa ga gwamnatin Tinubu, yana mai nuni da abin da ya bayyana a matsayin sauye-sauye masu kyau da ke shafar yankin Kudu-maso-gabas.

“Shugaba Tinubu mutum ne mai zurfin tunani, jarumi kuma mai kishin ƙasa. Muna da yaƙinin zai kawo gagarumin sauyi ga Nijeriya da yankin Kudu-maso-gabas,” inji shi.

Gwamnan ya kuma buƙaci abokan hamayyar sa na siyasa a Anambra da su ajiye bambance-bambancen su su haɗa kai domin cigaban jihar.

Ya ƙara da cewa duk da cewa fafatawar siyasa a jihar ta ƙare, ya kamata a mayar da hankali yanzu kan mulki nagari.

A nasa jawabin, Shettima ya yaba da jagorancin Soludo, yana mai bayyana shi a matsayin bawan jama’a wanda ke aiki bisa tunani da gaskiya.

Mataimakin Shugaban Ƙasar ya jaddada shirye-shiryen Gwamnatin Tarayya na yin aiki tare da gwamnatin Jihar Anambra, yana mai cewa ya kamata mulki ya fi mai da hankali kan jin daɗin al’umma fiye da siyasar jam’iyya.

Shettima ya kuma buƙaci mazauna jihar da su mara wa ƙoƙarin gwamnati baya na mayar da Anambra cibiyar tattalin arziki da zuba jari a Nijeriya.



 

No comments