Wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya ɗauki hankalin jama’a bayan da ya nuna yadda wani mutum ya bankaɗo zargin yunƙurin damfara ...
Wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya ɗauki hankalin jama’a bayan da ya nuna yadda wani mutum ya bankaɗo zargin yunƙurin damfara daga wata ma’aikaciyar gidan mai, wadda ake zargi da fara sayar masa da fetur daga mitar da ba a mayar sifili ba.
A cewar mutumin, ya nemi a sayar masa da fetur na naira dubu ashirin (N20,000), amma sai ya lura cewa mitar famfon ta riga ta nuna N5,501 tun kafin a fara zuba man. Nan take ya ƙalubalanci ma’aikatan, yana zargin cewa ba su sake saita mitar zuwa sifili ba, kuma ba su sanar da shi ba kafin fara zubawa.
Ba tare da ma’aikatan sun sani ba, mutumin yana ɗaukar duk abin da ke faruwa ta hanyar tabarau na zamani na Meta da ke iya ɗaukar bidiyo. Daga bisani, wannan hoton bidiyo ya zama hujja yayin muhawarar da ta kaure tsakaninsa da ma’aikatan gidan man.
A nata bangaren, ma’aikaciyar ta musanta zargin, tana mai cewa mitar famfo tana fara ne daga sifili, kuma duk wani adadi da ya rage a baya zai goge kai tsaye da zarar an latsa na’urar zuba mai. Sai dai mutumin ya ƙaryata wannan bayani ta hanyar nuna bidiyon da ya ɗauka, wanda ya nuna mitar na nan a kan N5,501 kafin a fara zuba man.
Wani ma’aikacin gidan man ya goyi bayan abokiyar aikinsa, yana mai cewa an zuba cikakken fetur na N20,000, kuma kuskuren da aka yi kawai shi ne rashin sanar da abokin ciniki adadin da mitar ta fara da shi lokacin da aka ɗauki bututun famfon.
Sai dai mutumin bai gamsu da waɗannan bayanai ba, inda ya buqaci a cire man da aka riga aka zuba daga motarsa. Ma’aikatan kuwa sun ƙi amincewa, suna nanata cewa an kammala cinikin yadda ya kamata.
Rikicin ya ƙara qamari lokacin da mutumin ya nemi ganin manajan gidan man. Bayan an sanar da shi cewa babu shugabanni a wurin a lokacin, sai ya yanke shawarar jira a cikin motarsa har sai wani mai iko ya iso domin warware matsalar, yana mai cewa ba zai yarda a cutar da shi ba.
Lamarin ya jawo muhawara mai zafi a kafafen sada zumunta, inda wasu ke ganin cewa damfara ce ƙarara, yayin da wasu ke cewa matsalar na iya kasancewa kuskuren fahimta ko rashin bayani ga abokin ciniki. Duk da haka, da dama sun yi kira ga masu sayen fetur su riƙa tabbatar da cewa an mayar da mitar famfo sifili kafin a fara zuba mai, domin kauce wa irin wannan taƙaddama.

No comments