Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnonin Arewa Sun Yi Tir Da Harin Bam A Maiduguri, Sun Nemi Ɗaukan Matakin Gaggawa

Daga Khalid Idris Doya  Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya yi Allawadai da fashewar jerin bama-bamai masu...

Daga Khalid Idris Doya 

Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya yi Allawadai da fashewar jerin bama-bamai masu muni da suka girgiza Maiduguri a ranar Litinin, inda ya bayyana harin a matsayin na rashin imani, na ta'addanci a kan fararen hula.

Rahotanni sun nuna cewa tashin jerin bama-bamai waɗanda wasu 'yan ƙunar baƙin wake suka aiwatar sun tashi ne a lokaci guda da yammacin ranar Litinin a kasuwar Maiduguri Monday Market, kofar shiga asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri (UMTH) da kuma Post- Office flyover dukka a Maiduguri babbar birnin jihar Yobe. 

'Yansanda sun ce mutane 23 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu sama da 100 suka jikkata.  

A cikin sanarwar da ya fitar a matsayinsa na Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana matuƙar jimami da alhininsa kan wannan mummunan hare-haren, tare da miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga gwamnati da al’ummar Jihar Borno, musamman iyalan waɗanda suka rasa 'yan uwansu.

Inuwa wanda kuma shi ne gwamnan jihar Gombe ya ce, "Wannan mummunan aika-aikar na tashin hankali ba wai kawai abin ƙyama ba ne, wani yunƙuri ne na zalunci da nufin haifar da tsoro da kuma kawo cikas ga zaman lafiyar da ake ƙoƙarin dawo da shi a yankin Arewa maso Gabas."

Sanarwar da Isma’ila Uba Misilli, Darakta-Janar na harƙoƙin yaɗa labarai na gidan jihar gwamnatin Gombe ya sanya wa hannu, Gwamna Inuwa ya ce, dole ne a yi Allah-wadai da hare-haren.

Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa ya jajanta wa waɗanda ke kwance a asibiti a halin yanzu domin samun kulawar likitoci sakamakon raunuka da suka samu a hare-haren, tare da yi musu addu'ar samun sauƙi cikin gaggawa.

Kazalika, ya kuma yaba wa jami'an agajin gaggawa da hukumomin tsaro kan yadda suka gaggauta ɗaukar mataki wajen shawo kan halin da aka shiga bayan fashe-fashen.

Ya sake jaddada ƙudurin gwamnonin Arewa na ci gaba da aiki kafaɗa-kafaɗa da Gwamnatin Tarayya da kuma hukumomin tsaro domin yaƙar dukkan nau’o’in ta’addanci da ayyukan laifi da ke barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyyar arewa maso gabas.

Inuwa ya buƙaci mazauna al'ummar Maiduguri da sauran yankunan da suke shiyyar da su kwantar da hankulansu, su kasance masu ci gaba da bin doka da oda, tare da bada cikakken haɗin kai da hukumomin tsaro ta hanyar bayar da sahihan bayanai da za su taimaka wajen binciken da ake yi da kuma taimaka musu a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso domin daƙile ayyukan ta'addanci. 

"A halin yanzu fiye da kowane lokaci, wajibi ne mu tsaya tsayin daka tare domin yaƙar maƙiyan zaman lafiya. Ba za mu yi ƙasa a guiwa kan yunƙurinmu na dawo da zaman lafiya a shiryar arewa maso gabas ba, tare za mu kawo ƙarshen wannan matsalar tsaron," ya jaddada.

Gwamna Inuwa Yahaya ya yi addu’ar Allah ya jiƙan waɗanda suka rasa rayukansu a wannan hare-haren, tare da kira ga hukumomin tsaron da su ƙara zage damtse domin ganin an kamo waɗanda suka aikata wannan mummunan aika-aikar kuma a hukunta su cikin gaggawa.
 

No comments