Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Shugaba Tinubu Ya Ƙaddamar Da Kwamitin GAMCO Domin Farfado Da Bangaren Wutar Lantarki

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da wani kwamitin mutane 11 da zai jagoranci kafa kamfanin Grid Asset Management Company Limited ...

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da wani kwamitin mutane 11 da zai jagoranci kafa kamfanin Grid Asset Management Company Limited (GAMCO), wani shiri da gwamnati ke ganin zai taimaka wajen magance matsalolin da suka addabi bangaren wutar lantarki a Nijeriya. Kafuwar kwamitin ta biyo bayan amincewar Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) a zamanta na ranar Laraba kan kafa kamfanin domin inganta sarrafa tsarin wutar lantarki da kuma rage matsalar wutar da ke yawan lalacewa.

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, wanda ya kaddamar da kwamitin a madadin shugaban kasa ranar Juma’a, ya bayyana cewa kafa GAMCO na daga cikin manyan matakan sauyi da gwamnatin Tinubu ke dauka domin farfado da bangaren wutar lantarki. Ya ce manufar ita ce inganta samar da wuta, musamman a bangaren 'grid' da tsarin isar da wuta, tare da tabbatar da cewa Najeriya ta amfana da dukkan karfin wutar da take da shi.

A cewarsa, kwamitin zai duba dokoki, ka’idoji da manufofin da ke tafiyar da samar da wutar lantarki daga samarwa zuwa rarrabawa da kuma kasuwar wutar lantarki. Haka kuma zai nazarci tasirin dokokin gyaran bangaren wutar lantarki na 2025, tare da gano duk wani sabani ko tangarda oda ka iya tasowa tsakanin tsarin GAMCO da dokoki da ka’idojin da ake da su a yanzu.

Kwamitin zai kuma binciki matsayin kadarori da yarjejeniyoyin Niger Delta Power Holding Company (NDPHC) da kuma ayyukan National Integrated Power Project (NIPP), musamman tashoshin wutar lantarki na Omotosho, Olorunshogo da Ihovbor, wadanda za su kasance matakin farko na aikin kamfanin. Bugu da kari, za su duba alakar ayyukan GAMCO da nauyin da dokar ta dora wa Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC), tare da nazarin tasirin kudi da kasuwa, ciki har da batun tallafin gwamnati da kudaden shiga.

Kwamitin yana karkashin jagorancin Femi Gbajabiamila a matsayin shugaba, yayin da Ministan Shari’a, da ministocin Wuta, Ayyuka, da Kudi suke cikin mambobi. Sauran sun hada da ministocin Sadarwa, Kimiyya da Fasaha, Sufurin Jiragen Sama, ƙaramin Ministan Man Fetur, Shugaban Hukumar Haraji ta Najeriya, da kuma masani a fannin makamashi Farfesa Yemi Oke. Dr. John Chidiebere Ezeamama, sakataren ma’aikatar harkokin majalisar zartarwa, shi ne sakataren kwamitin.

Sabon kamfanin GAMCO zai mayar da hankali kan farfado da wutar da ke makale a tsarin samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da hanyar wutar Benin zuwa Legas a matsayin matakin gwaji. Gwamnati na sa ran kamfanin zai iya dawo da akalla megawatt 1,600 na wuta cikin watanni 18 zuwa 24, tare da gina sabuwar babbar tashar wutar lantarki mai karfin 330KV a wannan yankin.

Gwamnatin tarayya ce za ta mallaki kamfanin gaba daya ta hannun ma'aikatar kuɗi (Ministry of Finance Incorporated), yayin da ake sa ran nasarar matakin gwajin zai zama tubalin fadada tsarin zuwa sauran yankuna na kasar domin tabbatar da daidaiton wutar lantarki, karfafa masana’antu, jawo zuba jari da kuma inganta rayuwar al’ummar Najeriya, daidai da manufofin Renewed Hope Agenda na gwamnatin Tinubu.
 

No comments