Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da tura sabbin Jakadu 65 na Nijeriya zuwa ƙasashe daban-daban na duniya da kuma Majalisar Dinkin...
Sanarwar da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Juma’a ta bayyana cewa Jakadun sun haɗa da ma’aikatan diflomasiyya 31 (career ambassadors) da kuma waɗanda ba ma’aikatan diflomasiyya ba 34 (non-career ambassadors).
Majalisar Dattawa ta riga ta tabbatar da sunayen jakadun a watan Disambar bara.
Daga cikin waɗanda aka tura akwai:
Senata Grace Bent – Jakadiya a Lome, Togo
Sanata Ita Enang – Jakada a Afirka ta Kudu
Victor Ikpeazu – Spain
Nkechi Linda Ufochukwu – Tel Aviv, Isra’ila
Mahmud Yakubu – Qatar
Reno Omokri – Mexico
Aminu Dalhatu – Babban Kwamishina a Birtaniya
Janar Abdulrahman Bello Dambazau mai ritaya – China
Lateef Kayode Are – Amurka
Femi Fani-Kayode – Jamus
Yakubu N. Gambo – Saudiyya
Jimoh Ibrahim – Babban Wakilin Nijeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya.
A bangaren jakadun ma’aikatan diflomasiyya kuwa, gwamnati ta tura su zuwa kasashe daban-daban ciki har da:
Mohammed Mahmud Lele – Algeria
Ahmed Mohammed Monguno – Masar
Muhammad Saidu Dahiru – India
Abdussalam Habu Zayyad – Senegal
Shehu Ilu Barde – Ghana
Aminu Nasir – Ethiopia
Haidara Mohammed Idris – Netherlands
Bako Adamu Umar – Morocco
Sulu Gambari Olatunji Ahmed – Malaysia
Ibrahim Danlami – Kenya
Adebayo Emmanuel Ayeni – Belgium
Wahab Adekola Akande – Switzerland
Bello Dogon-Daji Haliru – Thailand, da sauransu.
Sanarwar ta kara da cewa Birtaniya ta riga ta bayar da amincewar diflomasiyya (agrément) ga Babban Kwamishinan Najeriya mai jiran gado, Aminu Dalhatu.
Haka kuma Faransa ta amince da Ayo Oke a matsayin Jakadan Nijeriya a ƙasar.
Ma’aikatar Harkokin Waje ta sanar da sauran kasashen da aka tura jakadun zuwa, tare da neman amincewarsu kamar yadda tsarin diflomasiyya ya tanada.
Shugaba Tinubu ya kuma umarci ma’aikatar da ta gaggauta shirya shirin horaswa (induction programme) ga dukkan jakadun kafin su kama aiki a ofisoshin jakadancin Nijeriya a faɗin duniya.

No comments