Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sama Da Manyan Lauyoyi 100 Na Fuskantar Shari’o’in Cin Hanci A Nijeriya

Shugaban Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC), Ola Olukoyede, ya bayyana cewa a halin yanzu akwai aƙalla manya...



Shugaban Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC), Ola Olukoyede, ya bayyana cewa a halin yanzu akwai aƙalla manyan lauyoyi sama da 100 a Nijeriya da ke fuskantar tuhuma a kotu kan laifuffukan da suka shafi cin hanci da rashawa, lamarin da ya sake tayar da damuwa kan yadda ake karya ƙa’idojin aikin lauya a ƙasar.

Olukoyede ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Abuja yayin da yake jawabi a taron lacca na shekara-shekara karo na biyu na Kungiyar Body of Benchers, taron da ya hada manyan lauyoyi da masu ruwa da tsaki a bangaren shari’a.

Shugaban EFCC ya nuna damuwa kan yadda wasu daga cikin lauyoyi ke kara shiga cikin aikata laifuffukan kudi, yana mai gargadin cewa irin wannan hali na iya lalata martabar tsarin shari’a na kasa.

A cewarsa, hukumar yaki da cin hanci ta samu korafe-korafe da dama daga jama’a da ke zargin wasu lauyoyi da aikata damfara da sauran laifuffukan da suka shafi kudade.

Ya ce hukumar ta duba bayanan da ke cikin kundin bayananta, inda aka gano cewa kusan manyan lauyoyi 100 ne a halin yanzu ake gurfanar da su a kotuna kan laifuffukan da aka gano a yayin bincike.

Olukoyede ya bayyana cewa daga cikin zarge-zargen da ake yi musu akwai karkatar da kudaden kwastomomi, da kuma taimakawa wajen gudanar da safarar kudaden da ba a san asalin su ba, wato abin da ake kira money laundering.

Ya kara da cewa magance irin wannan matsala na buƙatar hadin kai tsakanin hukumomin yaƙi da cin hanci da shugabannin kungiyoyin lauyoyi domin tsaftace sana’ar shari’a.

A wajen taron kuma, Kwamitin Ladabtar da Lauyoyi (Legal Practitioners Disciplinary Committee) ya gabatar da rahotonsa na shekarar 2025, inda aka bayyana matakan ladabtarwa da aka dauka kan wasu lauyoyi da aka samu da laifin karya ka’idojin sana’arsu.

Da yake gabatar da rahoton, Babban Lauyan Najeriya (Senior Advocate of Nigeria), Onyechi Ikpeazu, ya ce binciken da aka gudanar ya tabbatar da cewa lauyoyi 17 sun aikata abubuwan da suka saba da ka’idojin sana’ar lauya yayin gudanar da aikinsu.

A cewarsa, laifuffukan da aka tabbatar sun fada cikin abin da ake kira “mummunar dabi’a yayin gudanar da aikin lauya.”

Ikpeazu ya bayyana cewa hukuncin da aka dauka kan wadannan lauyoyi ya bambanta daga cire suna daga rajistar lauyoyi gaba daya zuwa dakatar da su na wasu shekaru daga aikin lauya.

Ya ce lauyoyi uku daga cikinsu an cire sunayensu gaba daya daga rajistar lauyoyi, uku kuma an dakatar da su na tsawon shekaru biyar, yayin da biyu aka dakatar na shekaru hudu.

Sauran biyar an dakatar da su na shekaru uku, hudu kuma na shekaru biyu, yayin da aka gargadi lauya guda daya kawai.

A nasa bangaren, Shugaban Kungiyar Body of Benchers kuma tsohon Babban Alkalin Alkalan Nijeriya (Chief Justice of Nigeria), Mai Shari’a Kayode Ariwoola, ya ce an shirya taron laccar ne domin ba da dama ga lauyoyi su sake nazarin ɗabi’u, ƙa’idoji da martabar sana’ar su.

Ya jaddada cewa taron ba kawai bikin haduwa ba ne, illa wata dama ce ta tunani da sake duba darajar da sana’ar lauya ke da ita a cikin al’umma.

Haka kuma, Babbar Alƙalin Alƙalan Nijeriya, Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun, ta bayyana muhimmancin tsari da ladabtarwa wajen tabbatar da mutuncin sana’ar lauya.

Ta ce aikin Body of Benchers bai tsaya ga karbar sabbin lauyoyi cikin sana’ar lauya ba kawai, har ma yana da alhakin tabbatar da bin ka’idojin sana’a da kuma kare amincewar jama’a da tsarin shari’a na Nijeriya.

Kungiyar Body of Benchers ita ce babbar hukuma mafi ƙololuwa da ke kula da shigar da lauyoyi cikin sana’ar lauya tare da ladabtar da su idan suka karya dokokin sana’ar a Nijeriya.

No comments