Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta amince da aiwatar da wani sabon shiri na Exit Benefit Scheme, wanda zai bai wa ma’aikatan Gwamnatin T...
Shirin, wanda zai fara aiki daga ranar 1 ga Janairu, 2026, ana sa ran zai inganta matuƙa fa’idojin ritaya ga jami’an da suka yi wa ƙasa hidima na aƙalla shekaru 10 a aikin Gwamnatin Tarayya.
Tsarin yana daga cikin muhimman sauye-sauyen jin daɗin ma’aikatan gwamnati a ‘yan shekarun nan, kuma yana nuna ƙoƙarin gwamnati na tabbatar da cewa ma’aikatan gwamnati suna yin ritaya tare da ingantaccen tsaro na kuɗi.
An bayyana wannan cigaba ne a wannan Alhamis ɗin cikin wata sanarwa da Daraktan Hulɗa da Jama’a a Ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Eno Olotu, ya sanya wa hannu.
A cewar sanarwar, sabon tsarin zai bai wa ma’aikatan Gwamnatin Tarayya da za su yi ritaya giratuti da ya yi daidai da jimillar dukkan albashin da suke samu na shekara guda.
An tsara wannan manufa ne domin ƙarfafa tsarin jin daɗin ma’aikatan gwamnati tare da samar musu da ƙarin kariya ta kuɗi a ƙarshen aikin su.
Jami’ai sun bayyana cewa shirin zai shafi ma’aikatan Gwamnatin Tarayya da ke aiki a ma’aikatun da baitulmali ke ɗaukar nauyin su, sassan gwamnati masu zaman kan su daga ma’aikatu (extra-ministerial departments), da kuma hukumomin gwamnati.
Amincewar ta biyo bayan tattaunawa da shawarwari da aka shafe watannin ana yi da wani Kwamitin Fasaha na Ma’aikatun Gwamnati da dama (Inter-Ministerial Technical Committee) da Ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya ya kafa.
Kwamitin ya yi aiki tare da wasu cibiyoyin gwamnati da dama, ciki har da Hukumar Kula da Fansho ta Ƙasa, Ofishin Kasafin Kuɗi na Tarayya, da kuma Ofishin Akanta Janar na Tarayya.
Waɗannan hukumomi sun haɗa kai wajen samar da tsarin da zai tabbatar da cewa shirin mai ɗorewa ne, tare da ba da gagarumin tallafin kuɗi ga ma’aikatan da za su yi ritaya.
Jami’an gwamnati sun bayyana cewa Exit Benefit Scheme ba zai maye gurbin tsarin fansho na yanzu ba, sai dai ƙarin inganta tsarin Contributory Pension Scheme da aka fara a shekarar 2004.
A ƙarƙashin sabon tsarin, ma’aikatan gwamnati da suka cancanta za su karɓi giratuti ɗin tare da kuɗin fansho, wanda hakan zai ƙara inganta dukkan ƙunshin fa’idodin ritayar su.
Ana sa ran wannan shiri zai samar da ingantaccen tsaro na samun kuɗin shiga ga tsofaffin ma’aikatan gwamnati, tare da rage rashin tabbas na kuɗi bayan sun bar aikin gwamnati.
Da take mayar da martani kan wannan hukunci, Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Didi Walson-Jack, ta bayyana amincewar a matsayin babban muhimmin mataki a tarihin aikin gwamnati a Nijeriya.
Ta ce wannan manufa na nuna ƙudirin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na girmama sadaukarwa da jajircewar ma’aikatan gwamnati.
Ta ce: “Wannan amincewa wata babbar shaida ce ta yadda gwamnati ke daraja gagarumar gudunmawar ma’aikatan gwamnati, waɗanda suka sadaukar da shekarun su mafi ƙwazo wajen yi wa jama’a hidima da kuma cigaban ƙasa.”
Walson-Jack ta ƙara da cewa shirin zai inganta fa’idojin ritaya sosai, tare da ƙara ƙarfafa amincewar ma’aikata ga ƙudirin gwamnati na kula da jin daɗin su.
A cewar ta, manufar ta kuma yi daidai da gyare-gyaren da ake yi yanzu domin gina aikin gwamnati da ya fi inganci, kuzari, kuma mai mayar da hankali kan sakamako.
Ta tabbatar da cewa cikakkun ƙa’idojin yadda za a aiwatar da shirin za a sanar da su ga ma’aikatu da hukumomin da abin ya shafa nan gaba.
Wannan cigaba ya fi ɗaukar hankali musamman saboda ya zo shekaru 22 bayan ƙaddamar da tsarin fansho na Contributory Pension Scheme, wanda a wancan lokacin ya maye gurbin tsohon tsarin giratuti.
Sabuwar amincewar da Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta bayar yana nuna sabon yunƙuri na Gwamnatin Tarayya wajen inganta jin daɗin ma’aikatan ta, tare da ƙarfafa sauye-sauyen da za su tabbatar da makomar aikin gwamnati a Nijeriya.

No comments