Daga Ibrahim Muhammad, Kano Ɗan majajisar tarayya mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Fagge a jihar Kano, Hon. Barista Muhammad Bello Shehu Fagge ...
Ɗan majajisar tarayya mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Fagge a jihar Kano, Hon. Barista Muhammad Bello Shehu Fagge ya ƙara jaddada matsayin sa na ci gaba da goyon bayan Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sunusi.
Ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabi a madadin 'yan majalisar tarayya na jihar Kano a lokacind da Sarkin Kano ya kai ziyarar al'ada ta hawan Nasarawa a gidan Gwamnatin jihar Kano ranar Lahadi, wanda kuma ya sami tarbar Shugaban majalisar dokokin jihar Kano, Hon. Jibrin Isma'il Falgore da sauran muƙarraban Gwamnati a madadin Gwamna Abba Kabir Yusuf .
Hon. Muhammad Bello Shehu ya yi wa sarkin Kano barka da sallah da addu'ar Allah ya sa ibadu da aka yi karbabbu ne.
Hon. Fagge ya ce, "Mu dai a bangaren mu na majalisar tarayya, mai Martaba Sarki, sanin ka ne dubu bisa dubu muna kan tsarin layi na wannan gida mai albarka".
Tun da farko sai da Hon. Fagge ya bayyana ra'ayin sa na yin fatan Allah ya sa uku ta koma biyu ga Shugaban majalisar Dokokin jihar Kano, Hon. Jibrin Isma'il Falgore.

No comments