Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jigo a jam'iyyar APC a jihar Kan, Hon. Salihu Tanko Yakasai, wanda ake wa laƙabi da 'Ɗawisun Kanawa'...
Jigo a jam'iyyar APC a jihar Kan, Hon. Salihu Tanko Yakasai, wanda ake wa laƙabi da 'Ɗawisun Kanawa' ya bayyana ficewar sa daga jam’iyyar APC tare da komawar sa jam’iyyar ADC, inda ya ce ya ɗauki matakin ne bayan shawarwari da tuntuba da 'yan uwa da abokan arziki .
Tuntuni dai Hon. Yakasai ya mikƙa takardar ficewar sa daga jam’iyyar APC, tare da kammala rajista a sabuwar jam’iyyar da ya koma ta ADC, wanda hakan ya nuna cikakken sauyin sa a fagen siyasa.
Haka kuma Hon. Salihu Tanko Yakasai ya yi kira ga masu sha’awar shiga jam’iyyar ADC da su yi amfani da damar yin rijista ta yanar gizo cikin sauƙi domin tsarin rajistar yana ba da damar samun katin zama ɗan jam’iyya cikin ƙanƙanin lokaci.
Ya ce duk me sha’awar shiga jam’iyyar ta ADC zai iya yin rijista hatta ta wayar hannu cikin sauƙi a cikin ƙanƙanin lokaci zai samu katin sa na ɗan jam’iyya.
Shi dai Hon. Salihu Tanko Yakasai ya kasance daga cikin makusanta na tsohon Gwamnan jihar Kano, tsohon shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.
Hon. Salihu Tanko Yakasai ya bayyana cewa, "kamar yadda kowa ya sani, na zauna a PRP har aka kammala zabe da ni. Haka ma a wannan karon na shiga ADC, ni da jama'a ta, saboda rashin jin daɗin yadda Gwamnatin Tinubu ke tafiyar da mulkin ta, musamman mu a Arewa yadda yake nuna mana wariyar launin fata da halin ko-in- kula.

No comments