Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce kafafen yaɗa labarai suna taka muhimmiyar rawa wajen gina fahimtar jama’...
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce kafafen yaɗa labarai suna taka muhimmiyar rawa wajen gina fahimtar jama’a, ƙarfafa ɗaukar nauyin abin da ka aikata, da kuma jagorantar alƙiblar ƙasa.
Idris ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Abuja a lokacin wani taron wayar da kai ga kafafen yaɗa labarai kan yaƙi da halatta kuɗaɗe ta haramtacciyar hanya da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci (AML/CFT).
Babban Sakataren Hukumar Kula da Ayyukan Jarida ta Nijeriya, Dakta Dili Ezughah, shi ne ya wakilci ministan.
A jawabin sa, Ministan ce: “Kafafen yaɗa labarai ba 'yan kallo kawai ba ne; suna taka muhimmiyar rawa wajen gina fahimtar jama’a, ƙarfafa ɗaukar nauyin abin da mutum ya aikata da kuma tasiri a alkiblar ƙasa. Ta hanyar sahihan rahotanni, binciken jarida mai zurfi da kuma wayar da kai, suna ƙarfafa jama’a tare da taimaka wa yaƙi da cin hanci da rashawa.”
Ministan ya ce gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu tana ɗaukar matakai na musamman domin yaƙi da cin hanci da rashawa da kuma haramtattun kuɗaɗe.
Ya ƙara da cewa gyare-gyaren da aka aiwatar sun ƙarfafa tsarin tattara bayanan kuɗi, sun inganta sa ido kan hadahadar kuɗi masu alamar tambaya, tare da ƙara bin ƙa’idojin duniya.
Idris ya kuma nuna rawar da muhimman hukumomi suke takawa, ciki har da Hukumar Tattara Bayanai kan Harkokin Kuɗi ta Nijeriya, yana mai cewa ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomi ya taimaka wajen ganowa da kuma daƙile laifukan kuɗi.
Idris ya ce: “A matakin yankuna, Nijeriya tana aiki tare da ƙasashen Yammacin Afrika wajen yaƙi da laifuffukan kuɗi da ke wuce iyakokin ƙasashe.”
Ya ƙara da cewa gyare-gyaren da aka yi a ɓangaren kuɗi, tare da goyon bayan Babban Bankin Nijeriya, suna taimakawa wajen inganta gaskiya da dawo da aminci a tattalin arziki.
Ministan ya amince da ƙalubalen da kafafen yaɗa labarai suke fuskanta, ciki har da wahalar rahoton laifuffukan kuɗi, yaɗa bayanan ƙarya, ƙarancin kayan aiki da kuma matsalolin tsaro.
Ya yi kira da a ƙara haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da ’yan jarida tare da bunƙasa ƙwarewar su.
Ya ce: “Yaƙi da cin hanci da rashawa nauyi ne a wuyan kowa. Gwamnati da kafafen yaɗa labarai ba za su iya yin shi su kaɗai ba. Amma idan muka haɗa kai, za mu iya gina Nijeriya inda gaskiya ta zama ruwan dare kuma cin hanci da rashawa ba su da wurin ɓoyewa.”

No comments