Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Nijeriya Ta Yi Karin Haske Kan Yarjejeniyar Hijira Da Birtaniya

Fadar Shugaban Ƙasa ta yi karin haske kan yarjejeniyar haɗin gwiwa kan harkar hijira tsakanin Nijeriya da Birtaniya, bayan yawaitar bayanan ...


Fadar Shugaban Ƙasa ta yi karin haske kan yarjejeniyar haɗin gwiwa kan harkar hijira tsakanin Nijeriya da Birtaniya, bayan yawaitar bayanan da ake yaɗawa na ƙarya a wasu kafofin watsa labarai da sada zumunta.

A cikin sanarwar da mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce yarjejeniyar da aka ƙulla a lokacin ziyarar aiki ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu zuwa Birtaniya na da nufin ƙarfafa dangantaka da kuma tsara hanyoyin zirga-zirgar jama’a cikin tsari mai kyau.

~ Ba a tilasta Nijeriya karɓar baƙin haure ba

Sanarwar ta jaddada cewa babu wani sashe a cikin yarjejeniyar da ke tilasta Nijeriya ta karɓi baƙin haure waɗanda ba ‘yan ƙasar ba. Ta ce duk wanda za a dawo da shi dole ne ya kasance ɗan ƙasar da aka tabbatar da asalinsa ta hanyoyi da dama na tantancewa.

Haka kuma, idan aka samu kuskure wajen mayar da mutum, ƙasar da ta turo shi ce za ta sake karɓarsa tare da ɗaukar dukkanin kuɗin da abin ya shafa.

~ Mayar da ‘yan ƙasa cikin mutunci

Yarjejeniyar ta tanadi cewa duk wani ɗan ƙasa da za a mayar daga wata ƙasa dole ne a yi hakan cikin mutunci, tare da kiyaye haƙƙoƙinsa na ɗan adam.

Hukumomin tsaro na ƙasashen biyu za su yi aiki tare domin kare lafiyar ‘yan ƙasa da kuma rage matsalolin da ka iya tasowa daga batun hijira.

~ Tsare-tsaren dawo da ‘yan ƙasa

An bayyana cewa za a iya dawo da mutum ta jirgin sama na yau da kullum ko na musamman, tare da bayar da cikakken bayani kafin kwanaki biyar da aiwatar da hakan.

Haka kuma, dole ne a tabbatar da sahihancin takardun tafiya, ko ta hanyar fasahar tantance bayanai (biometric), kafin a kammala shirin mayar da mutum.

~ Nijeriya ce ke da ikon bayar da takardu

Sanarwar ta fayyace cewa Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya ce kaɗai ke da ikon bayar da takardun da suka dace ga ‘yan ƙasar da za a dawo da su, ba tare da wani tsoma baki daga ƙasashen waje ba.

~ Tallafin sake tsugunar da masu dawowa

A cewar sanarwar, yarjejeniyar ta tanadi tallafi ga masu dawowa, ciki har da:
•    Taimakon gaggawa kamar masauki da sufuri
•    Haɗa su da iyalansu
•    Tallafin sana’o’i da ilimi
•    Samar da damar kafa kasuwanci

Haka kuma, za a samar da asusun tallafi domin taimaka wa masu dawowa su samu dogaro da kai a rayuwarsu.

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa irin wannan yarjejeniya ba sabuwa ba ce, domin an taɓa kulla makamanciyarta a shekarun baya, kuma wannan sabuwar yarjejeniyar za ta ɗauki tsawon shekaru biyar kafin a sabunta ta.

A ƙarshe, gwamnati ta buƙaci kafafen yaɗa labarai da su riƙa neman sahihin bayani kafin wallafa labarai, domin kauce wa yaɗa bayanan da ba su dace ba.
 

No comments