Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

ƘARAMAR SALLAH: Sarkin Musulmi Ya Gargaɗi Shugabannin Duniya Kan Hatsarin Yaƙe-Yaƙe

ƘARAMAR SALLAH: Sarkin Musulmi Ya Gargaɗi Shugabannin Duniya Kan Hatsarin Yaƙe-Yaƙe Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III,...

ƘARAMAR SALLAH: Sarkin Musulmi Ya Gargaɗi Shugabannin Duniya Kan Hatsarin Yaƙe-Yaƙe
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III, wanda kuma shi ne Shugaban Ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam, ya taya al’ummar Musulmin Nijeriya da na duniya baki ɗaya murnar kammala azumin watan Ramadan na shekarar 1447 bayan Hijira da kuma bikin Ƙaramar Sallah.

Ya bayyana cewa wannan lokaci ya kamata ya zama na zurfafa tunani kan ayyukanmu, tare da addu’ar samun zaman lafiya, kwanciyar hankali, farin ciki da albarka ga Musulmi da iyalansu.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Farfesa Khalid Abubakar Aliyu, Babban Sakataren Jama’atu Nasril Islam ya sanyawa hannu.

Sanarwa ta ce, Sarkin Musulmi ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki da Ya karɓi ibadun azumi da sauran ayyukan alheri da aka gudanar a watan Ramadan, tare da gafarta kurakuran da aka aikata. Haka kuma ya yi addu’ar Allah Ya ci gaba da saukar da rahamarsa a cikin watanni masu zuwa.

Ya tunatar da al’umma cewa Ubangijin watan Ramadan shi ne Ubangijin dukkan watanni, don haka wajibi ne Musulmi su ci gaba da tsoron Allah da riƙo da kyawawan halaye a kowane lokaci. Ya kuma ambaci ayar Alƙur’ani mai girma wadda ke cewa: “Ka bauta wa Ubangijinka har sai mutuwa ta zo maka.” (Suratul Hijr: 99).

Haka kuma ya ƙarfafa Musulmi da kada su manta da azumin kwanaki shida na watan Shawwal (Sittah Shawwal), wanda Manzon Allah (SAW) ya ƙarfafa yi bayan Ramadan.

Dangane da halin da ƙasa ke ciki, Sarkin Musulmi ya buƙaci al’ummar Musulmi su ƙara yawaita addu’o’i domin kare kai da al’umma daga duk wani bala’i, musamman ganin yadda zaɓen shekarar 2027 ke ƙaratowa. Ya kuma yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su yi nazari cikin zurfi tare da aiki tuƙuru domin tabbatar da zaɓe mai inganci, gaskiya da adalci.

Ya jaddada cewa babu yadda za a samu shugabanci nagari sai an fara da tabbatar da zaman lafiyar ƙasa.

A ɓangaren duniya kuwa, Sarkin Musulmi ya yi kira ga shugabannin ƙasashe da su rage tashin hankali da rikicin da ke tsakanin Iran da Amurka/Isra’ila, tare da sauran rikice-rikice a duniya, domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya baki ɗaya.

Ya bayyana cewa tarihi ya nuna yaƙe-yaƙe ba su haifar da alheri, sai dai lalacewar rayuka da tattalin arziki. Ya kuma yi gargaɗin cewa idan aka bari irin waɗannan rikice-rikice su ƙara tsananta, za su iya shafar samar da abinci da tattalin arzikin duniya, musamman ga ƙasashe masu rauni irin su Nijeriya.

A ƙarshe, Sarkin Musulmi ya sake taya Musulmi murnar Sallah, yana mai fatan zaman lafiya da albarka, tare da addu’ar Allah Ya karɓi azumin Ramadan da kuma ibadun da aka gudanar.
 

No comments