Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce babban taron jam’iyyar APC na ƙasa da za a yi zai nuna haɗin kai, ƙwarew...
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce babban taron jam’iyyar APC na ƙasa da za a yi zai nuna haɗin kai, ƙwarewar dimokiraɗiyya da kuma jajircewa wajen aiwatar da Shirin Sabunta Fata.
Idris ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Abuja a wajen taron manema labarai na duniya da jam’iyyar APC ta shirya gabanin babban taron ta na 8 da za a gudanar daga ranar 27 zuwa 28 ga Maris.
Ya bayyana taron a matsayin wani muhimmin mataki da zai haɗa wakilai daga jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya domin zaɓen shugabanni da tattauna manufofi.
Ya ce: “Wannan taro ba kawai na yau da kullum ba ne, lokaci ne na nazari, ƙarfafa haɗin kai da kuma tsara matakan gaba. Yana nuna ƙudirin mu na ƙarfafa dimokiraɗiyya, inganta tafiyar da jam’iyya da kuma daidaita manufofin jam’iyya da muradun cigaban ƙasa.”
Ministan ya ce taken taron, “Haɗin Kai a Cigaba – Ƙarfafa Shirin Sabunta Fata,” yana nuna jajircewar jam’iyyar wajen tabbatar da haɗin kai da kuma bin aƙidar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
A cewar sa, APC ta ci gaba da kasancewa jam’iyya mai ɗauke da manufofi na cigaba da haɗin kan ƙasa, tare da nuna ƙwarewa wajen tafiyar da sauyin shugabanci cikin tsari da lumana.
Ya ƙara da cewa an kammala dukkan shirye-shiryen da suka dace domin tabbatar da cewa taron zai gudana cikin tsari, gaskiya da inganci a dandalin Eagle Square da ke Abuja.
Ya ce: “A yayin da ake shirin gudanar da taron, APC tana sake jaddada haɗin kai da nauyin da ke kan ta. Wannan taro zai nuna jajircewar mu ga dimokiraɗiyya, bin ƙa’ida da kuma yanke shawara mai haɗa kowa.”
Idris ya yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa rawar da yake takawa wajen ƙarfafa jam’iyyar da kuma tafiyar da manufofin da ke bunƙasa cigaban ƙasa.








No comments