Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Wakilai 8,453 Za Su Halarci Babban Taron APC – Minista

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na Ƙasa, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana a taron manema labarai na APC na duniya da aka gudanar a Ab...

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na Ƙasa, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana a taron manema labarai na APC na duniya da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis cewa ana sa ran wakilai 8,453 za su halarci babban taron ƙasa mai zuwa na jam’iyyar APC, waɗanda aka zaɓo daga yankuna shida na siyasar ƙasar nan.

Ministan ya bayyana cewa taron zai nuna yadda jam’iyyar take haɗa kowa da kowa, haɗin kai, da kuma balagar dimokiraɗiyya, tare da ƙarfafa ƙudirin ta na inganta cigaban ƙasa a ƙarƙashin ajandar “Sabon Fata” ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu. 

Ya ce: “Muna sa ran wakilai 8,453 daga sassa daban-daban na ƙasar nan. Wannan ya nuna yadda jam’iyyar mu take da faɗin ƙasa, haɗin kai, da kuma ƙarfi a tsarin tafiyarta.”

Da yak amsa tambayoyin ’yan jarida a Abuja, ministan ya tabbatar da cewa an kammala dukkan shirye-shiryen da suka dace domin karɓar dukkan wakilan da aka tantance ba tare da an bar kowa a baya ba. 

Ya ce: “Ina tabbatar maku cewa babu wanda za a bari a baya. Jam’iyyar tana da sanin ya-kamata sosai, kuma kasafin kuɗin mu yana da tsarin da zai daidaita kansa domin ɗaukar nauyin dukkan wakilai.”

Idris ya kuma bayyana cewa zirga-zirgar wakilai da membobin kwamitoci daga sassa daban-daban na ƙasar nan ya gudana cikin sauƙi ba tare da wata matsala ba. 

Ya ƙara da cewa: “A halin yanzu, ba mu samu wani lamari ba, kuma ba ma sa ran hakan. Wannan na nuna yadda tsaro ke ƙara inganta da kuma yadda ake ci gaba da bunƙasa ababen more rayuwa a faɗin ƙasar nan.”

Ministan ya kuma bayyana cewa za a samar da cikakkiyar cibiyar yaɗa labarai a wurin taron domin tabbatar da samun bayanai cikin sauƙi, tare da bai wa dukkan kafafen yaɗa labarai da aka tantance damar yin rahoto. 

Ya ce: “Za a samar da cibiyar yaɗa labarai domin tabbatar da cewa ’yan Nijeriya sun samu cikakken bayani. Muna gayyatar dukkan kafafen yaɗa labarai, kuma za a ba su izini domin gudanar da aiki yadda ya kamata.”

Ya kuma buƙaci ’yan jarida da su kiyaye ƙa’idojin aiki da gaskiya a rahotannin su, yana mai cewa: “Yana da muhimmanci mu riƙa bayar da rahoto cikin gaskiya, adalci, da kuma amfani ga ƙasa, tare da tuna cewa Nijeriya ita ce a zuciyar duk abin da muke yi.”

Waɗanda suka halarta sun haɗa da Ministan Fasaha, Al’adu, Yawon Buɗe Ido da Tattalin Arzikin Kirkira, Hannatu Musawa; Ministan Sufurin Jiragen Sama da Bunƙasa Sararin Samaniya, Festus Keyamo; mataimakin shugaban babban kwamiti, Pius Ayim; mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Cif Sunday Dare; mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan bayanai da dabaru, Mista Bayo Onanuga; da sauran manyan jigajigan jam’iyyar.
 

No comments