Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Tarayya Ta Fara Rijistar Horar da ‘Yan Nijeriya Miliyan 10 Kan Ilimin Kuɗi

Shirin zai ɗaga darajar Nijeriya a duniya – Shettima Gwamnatin Tarayya ta fara rijistar horas da ‘yan Najeriya miliyan 10 kyauta kan ilimin ...


Shirin zai ɗaga darajar Nijeriya a duniya – Shettima

Gwamnatin Tarayya ta fara rijistar horas da ‘yan Najeriya miliyan 10 kyauta kan ilimin hada-hadar kuɗi da shigar da jama’a cikin tsarin banki (financial inclusion).

Za a gudanar da rijistar ne ta hanyar ƙungiyar WAWUAfrica, wadda ke da manufar ƙarfafa mata da shugabanci a Afirka, ta shafin intanet na: http://wawuafrica.com/onboarding.

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ne ya ƙaddamar da fara rijistar a wani taron yanar gizo tare da Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Haɗa Jama’a da Tsarin Tattalin Arziƙi da Kuɗi (Presidential Committee on Economic and Financial Inclusion – PreCEFI) da sauran abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa.

An wakilce shi da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tattalin Arziƙi, Dr. Tope Fasua, inda ya bayyana cewa shirin zai zama ɗaya daga cikin manyan tsare-tsaren Bola Ahmed Tinubu da za su yi tasiri ga rayuwar ‘yan Najeriya da ma duniya baki ɗaya.

Ya ce shirin zai mayar da hankali kan fannoni kamar:

Ilimin fasahar zamani (Digital & IT literacy)

Ilimin kuɗi da tattalin arziƙi

Harkokin kasuwanci da sana’o’i

Kiwon lafiya da walwala

Fasaha da ƙirƙira (creative arts)

Sana’o’in hannu da injiniyanci

Baƙuncin yawon buɗe ido

Shettima ya yaba da haɗin gwiwar ƙungiyoyi irin su lWorld Bank) Bankin Duniya; (African Union) Ƙungiyar Tarayyar Afirka; (Economic Community of West African States) Ƙungiyar Tattalin Arziƙin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS); Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Ƙasa (National Information Technology Development Agency NITDA) tare da sauran abokan hulɗa wajen tabbatar da nasarar shirin.

A nasa bangaren, Mashawarci ga Shugaban Ƙasa kan harkokin tattalin arziƙi da shigar da jama’a cikin tsarin kuɗi, Dr. Nurudeen Zauro, ya gargadi ‘yan Najeriya da kada su biya ko sisi domin wannan horo, yana mai jaddada cewa shirin kyauta ne gaba ɗaya.

Ya ce: “Manufar ita ce a wayar da kan jama’a yadda za su yi rijista cikin sauƙi, ba tare da an yaudare su da biyan kuɗi ba.”

A cewarsa, ana kuma ƙoƙarin tabbatar da cewa dandalin rijistar yana da inganci, gaskiya da riƙon amana.

An tsara shirin ne musamman domin matasa da mata, domin su samu ƙwarewar kuɗi, dabarun saka jari da kuma ilimin zamani da zai taimaka wajen bunƙasa arzikinsu.

Haka kuma, a watan Fabrairun 2026, ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa ta hannun PreCEFI ya rattaba hannu kan yarjejeniya da manyan ƙungiyoyin ƙwararru guda shida, ciki har da ICAN, CIBN, CIS, NICA, CRMI da kuma NIIE, domin samar da tsarin horaswa, takardar shaida (certification), da kuma jagoranci ga mahalarta shirin.

Shirin na daga cikin matakan Gwamnatin Tarayya na rage talauci, ƙarfafa tattalin arziƙi da kuma inganta rayuwar al’umma a fadin ƙasar.
 

No comments