Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da faɗaɗa aikin Shirin Shugaban Ƙasa na Amfani da Iskar Gas (PiCNG) domin ya haɗa da motocin lan...
Bayan wannan amincewa, za a riƙa kiran shirin da suna PiCNG & EV, wanda zai kula da tsarawa da aiwatar da dabarun sufuri mai tsafta a faɗin ƙasar nan, wanda ya haɗa da motocin gas da na lantarki.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Alhamis a Abuja.
Sanarwar ta ce shirin zai ci gaba da bunƙasa samar da kayayyakin more rayuwa na gas (CNG), ciki har da tashoshin na’urorin cika gas, da kuma shirin sauya motocin man fetur zuwa gas a faɗin ƙasar.
Haka kuma, PiCNG & EV zai jagoranci shigar da motocin lantarki, gina tashoshin cajin motocin lantarki, da jawo zuba jari a fannin.
Onanuga ya bayyana cewa gas na da muhimmanci wajen rage kuɗin sufuri da ƙarfafa tsaron makamashi, la’akari da yalwar albarkatun gas da Najeriya ke da su.
Ya ƙara da cewa wannan mataki zai taimaka wajen rage kashe kuɗaɗen waje tare da gina tsarin sufuri mai ɗorewa.
A cewarsa, haɗa motocin lantarki cikin shirin na ƙara ƙarfafa manufofin gwamnati na samar da sufuri mai araha, inganci da kuma kare muhalli.
Shugaban ya kuma umarci Shugaban Hukumar PiCNG & EV, Ismaeel Ahmed, da ya gaggauta samar da tsari na rarraba kayayyakin sauya motocin zuwa gas a duk faɗin ƙasa.
Tinubu ya jaddada cewa dole ne a samar da kayayyakin cikin sauƙi kuma ba tare da tsadar da za ta yi wa jama’a nauyi ba.
Domin cimma hakan, shirin zai yi aiki tare da CreditCorp Nigeria da bankuna da sauran abokan hulɗa domin samar da hanyoyin biyan kuɗi masu sauƙi.
Haka kuma, Shugaban ya ba da umarnin ƙara yawan amfani da na’urorin cika gas masu motsi (MRUs), domin sauƙaƙa samun gas yayin da ake ci gaba da gina manyan tashoshi.
Ana sa ran wannan shiri zai taka muhimmiyar rawa wajen sauya tsarin sufuri a Najeriya zuwa wanda ya fi tsafta da dorewa.

No comments