Gundarin adadin kuɗaɗen ajiya na waje a Nijeriya ya ƙaru nunka sau bakwai da rabi, tsakanin 2023 zuwa ƙarshen 2025, inda ya kai dala biliyan...
Gundarin adadin kuɗaɗen ajiya na waje a Nijeriya ya ƙaru nunka sau bakwai da rabi, tsakanin 2023 zuwa ƙarshen 2025, inda ya kai dala biliyan $34.8 a shekarar da ta gabata.
Wannan adadi, wanda ke nuna ingancin ajiyar kuɗaɗen waje na ƙasa, ya kasance dala biliyan $3.99 kacal a ƙarshen shekarar 2023.
Gwamnan Babban Bankin Niieriya (CBN), Olayemi Cardoso, ne ya bayyana sabon adadin a cikin wata sanarwa.
An rawaito Cardoso na cewa wannan ci gaba yana nuna gagarumar ƙarfafuwa a mataki da kuma ingancin ajiyar kuɗaɗen waje na Nijeriya cikin shekaru uku da suka gabata.
Yayin da yake waiwaye kan abin da ya kira gagarumin ingantaccen tsarin ajiyar kuɗi, Cardoso ya bayyana cewa matsayin adadin kuɗaɗen a shekarar 2025 kaɗai ya zarce jimillar da aka samu a ƙarshen 2023, wanda ya tsaya a dala biliyan $33.22.
Ya ƙara da cewa adadin ya tashi daga dala biliyan $23.11 a ƙarshen 2024 zuwa dala biliyan $34.8 a ƙarshen 2025, yayin da asusun ajiyar kuɗaɗen waje da ke CBN shi kuma ya ƙaru daga dala biliyan $40.19 zuwa dala biliyan $45.71 a wannan lokaci, wanda ke nuna ƙarin dala biliyan $5.52.
Ya bayyana cewa wannan faɗaɗa ya nuna yadda ƙarfin Njeriya ya ƙaru wajen biyan basussukan waje, tallafawa daidaiton farashin canjin kuɗi, da kuma ƙarfafa juriya da daidaiton tattalin arziki baki ɗaya.
Cardoso ya bayyana matsayin ajiyar kuɗin ƙarshen 2025 a matsayin tabbaci mai ƙarfi ga nasarar gyare-gyaren manufofi da daidaita ɓangaren kuɗaɗen waje da bankin ke aiwatarwa.
Haka kuma, ya sake jaddada ƙudirin CBN na ci gaba da riƙe isasshen ajiyar kuɗi, tallafawa gudanar da kasuwar canjin kuɗi cikin tsari, ƙara amincewa da matsayin tattalin arzikin Nijeriya a waje, da tabbatar da ɗorewar tattalin arziki daidai da dokar da ta kafa bankin.
Ya cewa adadi da jimillar ajiyar kuɗaɗen waje na Nijeriya, sun nuna gagarumin ci gaba a ƙarshen 2025, wanda ke nuna ƙarfafa ginshiƙan ɓangaren waje da kuma ɗorewar gyare-gyaren manufofi.
Bayan ya bayyana hakan a taron bayan zaman Kwamitin Tsare-tsaren Kuɗi (MPC), inda ya ce ajiyar kuɗaɗen waje na ƙasa ya kai dala biliyan $50.45 zuwa ranar 16 ga Fabrairu, 2026, Cardoso ya jaddada cewa gundarin adadin ya nuna amfanin ƙara gaskatawa da amincin gudanar da harkokin canjin kuɗi, wanda ke ƙara yarda da masu zuba jari, jawo ƙarin shigowar kuɗaɗen waje da inganta hanyoyin sarrafa ajiyar kuɗi.

No comments