Daga Ibrahim Muhammad, Kano Tsohon Shugaban ƙungiyar masu fasahar gyaran Ababen hawa na Kasa, Nigerian Automobile Technicians Association (N...
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Tsohon Shugaban ƙungiyar masu fasahar gyaran Ababen hawa na Kasa, Nigerian Automobile Technicians Association (NATA), Jakadan ƙungiyar na ƙasa, Injiniya Dakta Magaji Muhammad Sani, ya yi kira ga 'yan kasuwa, musamman masu sayar da kayan masarufi da su sa tsoron Allah su guji yin amfani da watan Ramadan wajen neman riba da ta wuce kima.
A cikin zantawar sa da manema labarai, Magaji Sani ya ja hankalin mutane su ji tsoron Allah a duk abin da za su yi, ya kuma ce su zama mai É—orewa wajen yin ayyuka na kirki ko bayan watan Ramadan.
Ya kuma yi kira ga masu hali da masu muƙamai na mulki a kowane mataki su ƙara himma wajen taimaka wa marasa ƙarfi.
Magaji Sani ya ƙara yin kira ga al'umma su duƙufa su jajirce sosai wajen roƙon Allah a cikin wannan wata mai alfarma domin shi kaɗai ne mai iko da zai maganin dukkan matsaloli.
A ƙarshe ya ce, "mu nuna masa gazawar mu da halin da muke ciki a ƙasar nan, ba mu da yadda za mu yi, mafita na gare shi, mu roƙe shi ya taimake mu ya yaye mana halin da ake ciki na rashin zaman lafiya da ƙunchi a ƙasar nan."

No comments