Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Zan Yi Murabus Idan Aikin Hanyar Abuja–kaduna–kano Bai Yi Inganci Ba – Ministan Ayyuka

  Ministan Ayyuka, David Umahi, ya bayyana cewa a shirye yake ya ajiye muqaminsa idan aka tabbatar cewa aikin hanyar Abuja–Kaduna–Kano bai c...




Ministan Ayyuka, David Umahi, ya bayyana cewa a shirye yake ya ajiye muqaminsa idan aka tabbatar cewa aikin hanyar Abuja–Kaduna–Kano bai cika ƙa’idojin inganci ba.

Ya ce yana maraba da a gudanar da gwaje-gwaje masu zaman kansu domin tantance nagartar aikin.

Umahi ya yi wannan jawabi ne yayin da yake kare kasafin kuɗin ma’aikatarsa a gaban zaman hacin gwiwa na Majalisar Dokoki ta Ƙasa.

A zaman, wasu ‘yan majalisa sun nuna damuwa kan yadda aka ba wani vangare na aikin ga kamfani da suka ce ba a san shi sosai a fannin gine-ginen hanyoyi ba.

Sanata Adams Oshiomhole ya tambayi dalilin da ya sa aka karve aikin daga wani kamfani da aka saba da shi aka ba wani kamfani da ake alaaanta shi da harkar sayar da janareto. Ya ce bai dace a yi watsi da gogaggun kamfanoni ba.

Da yake mayar da martani, Umahi ya ce abin da ya kamata a fi mayar da hankali a kai shi ne ingancin aikin, ba tarihin kamfani ba. Ya ƙalubalanci ‘yan majalisar da su kawo kwararrun masu gwajin qanqare domin su duba aikin. “Idan aka gwada aka same shi da gazawa, zan yi murabus,” inji shi.

Ministan ya ƙara da cewa, matsalar lalacewar hanyoyi ba lallai ta ta’allaƙa ga ko an yi amfani da kwalta ko kankare ba, illa dai rashin kulawa da sa ido yadda ya kamata.

A wani bangare, Umahi ya soki tsarin sakin kuɗaɗen manyan ayyuka, yana mai cewa tsarin da Ma’aikatar Kudi ke bi na hana ayyuka tafiya yadda ya kamata. Ya ce sama da kashi 95 cikin 100 na ayyukan ma’aikatar na ci gaba da gudana, don haka ana buƙatar a rika sakin kudaden da wuri domin kammala su cikin lokaci.

Zaman ya samu ɗan hayaniya yayin da aka samu savani tsakanin ministan da wasu ‘yan majalisa, lamarin da ya kai ga musayar kalamai kafin daga bisani aka samu daidaito.

No comments