Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

CBN Ya Haramta Yin Furanni Da Kuɗin Naira

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ayyana amfani da abin da ake kira “money bouquet” wato shirya takardun kuɗi cikin siffar furanni a matsayin ...




Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ayyana amfani da abin da ake kira “money bouquet” wato shirya takardun kuɗi cikin siffar furanni a matsayin cin zarafin Naira, tare da jera shi cikin laifuffukan da suka haɗa da liƙi, murza kuɗi da sauran su.

Rahotanni sun ce wannan mataki na zuwa ne gabanin bikin Ranar Masoya ta bana da za a gudanar a ranar 14 ga Fabrairu, 2026, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta.

A ƙarƙashin dokar CBN, duk wanda aka kama yana lalata ko muzanta kuɗin ƙasa na iya fuskantar ɗaurin aƙalla watanni shida ko tarar da ba ta gaza Naira 50,000 ba.

Hukumomin sun buqaci ‘yan Nijeriya da su kare martabar Naira tare da kai rahoton duk wanda ya karya dokar, yayin da jami’an tsaro ke ƙara tsaurara matakai kan masu laifi a faɗin ƙasa.

Matakin ya shafi al’adar bai wa masoya kyautar kuɗi da aka naɗe su cikin siffar furanni, wanda ya zama ruwan dare a lokutan bukukuwa, musamman a ranakun aure da shagulgula.

Sai dai sanarwar ta haifar da rarrabuwar kawuna a shafukan sada zumunta. Wasu marasa aure sun nuna farin ciki, suna cewa matakin zai rage musu matsin lamba a lokacin soyayya. Wasu kuwa daga vangaren masoya sun nuna damuwa, suna cewa dokar ta zo a lokacin da mutane ke shirye-shiryen bikin soyayya.

Wasu masu sharhi sun yi barkwanci da cewa za su koma tura kuɗi ta hanyar canja wurin banki ko amfani da kuɗaɗen ƙasashen waje domin kauce wa hukunci. Wasu kuma sun ce duk wanda aka gani da “money bouquet” za su kai ƙarar sa ga hukuma.

Duk da cewa CBN bai fitar da sabon bayani na musamman kan ranar soyayya ba, dokokin bankin sun daɗe suna haramta duk wani abu da zai janyo lalacewar takardun kuɗi.

Yayin da ranar 14 ga Fabrairu ke ƙara matsowa, ana sa ran za a ga yadda wannan mataki zai shafi shagulgulan masoya a faɗin Nijeriya.

No comments