Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

'Yan Bindiga 10,000 Sun Tarwatsa Ƙauyuka A Bauchi, – Gwamna Bala Ya Nemi Tallafin Gwamnatin Tarayya

Daga Khalid Idris Doya  Aƙalla 'yan bindiga 10,000 masu ɗauke da muggan makamai sun kori tare da tarwatsa al’ummomi da dama a ƙaramar hu...

Daga Khalid Idris Doya 

Aƙalla 'yan bindiga 10,000 masu ɗauke da muggan makamai sun kori tare da tarwatsa al’ummomi da dama a ƙaramar hukumar Alkaleri da ke Jihar Bauchi.

Al'ummomin da abin ya shafa sun haɗa da Mansur, Digare, Yalo, Gwana, Futuk da sauran al’ummomi da ke kewaye da su.

Gwamna Bala Mohammed ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis lokacin da ya ziyarci mutanen da suka rasa matsugunansu da ke samun mafaka a babban makarantar Firamare ta Kashere, a ƙaramar hukumar Akko ta Jihar Gombe. Ya ce lamarin ya yi muni matuƙa inda ya nemi taimakon Gwamnatin Tarayya.

"Na zo nan ne domin jajanta wa mutanenmu daga wannan ɓangare na ƙaramar hukumar Alkaleri, wanda shi ne garina na haihuwa. Kwana biyu da suka gabata (Talata), na je Kafin Duguri inda 'yan bindiga suka mamaye wani ƙauye. Ina alfahari da cewa mutanenmu sun tsaya tsayin daka, sun yi jarumtaka wajen tinƙararsu, suka tilasta musu tserewa zuwa tsaunukan da ke kewaye," in ji gwamnan.

Sai dai ya nuna damuwa kan rahotannin sirri da ke nuni da cewa 'yan bindigar na sake haduwa a wani wuri da ake kira Dajin Madam a Alkaleri.

"Rahotannin sirri sun nuna suna ɗaukar sabbin mutane, daga cikin da wajen yankunanmu. Wasu daga cikin su na da alaƙa da ayyukan hakar ma’adanai ba bisa ƙa'ida ba da muka dakatar,” in ji shi.

Ya kara da cewa, “Al’ummomi kamar Mansur, Digare, Futuk, Yalo da Gwana da sauran kewayensu an fatattake su sakamakon mamayar ‘yan bindiga masu yawa, kusan 10,000. Ba abu ne mai sauƙi ga fararen hula marasa makamai, ‘yan banga ko ma jami’an tsaro su tunƙari irin wannan adadi ba."

Gwamnan ya ce zai ziyarci Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu domin neman umarni kai tsaye ga manyan hafsoshin soja da 'yan sanda don su ƙaddamar da wani samame na haɗin gwiwa mai ƙarfi a yankin domin shawo kan 'yan bindigan.

Ya ce, “Na san Shugaban Kasa shugaban kowa ne. Zan gana da shi gobe Insha Allah domin bayar da umarni ga manyan hafsoshin soja da ‘yan sanda domin mu yi ƙoƙari na bai-ɗaya a wannan yanki.”

Ya tabbatar da cewa jami’an tsaro na iya ƙoƙarinsu, kuma za a yi amfani da fasaha da bayanan sirri wajen gano miyagun mutanen.

Gwamna Mohammed ya kuma sanar da cewa Jihar Bauchi na shirin ɗaukar matasa kusan 2,000 cikin ‘yan banga, inda za a basu horo yadda ya kamata domin taimakawa wajen kare al’umma.

"Dole mu haɗa kai, Gwamnatin Tarayya, jami’an tsaro, shugabannin al’umma da jama’a domin kare garuruwanmu," in ji shi.

Ya ce za a yi tsarin samar wa al'ummomin da abun ya shafa makamai domin su yi tsayuwar daka wajen kare kansu. 

Ya buƙaci mazauna yankunan da aka tarwatsa su kasance masu juriya, yana mai tabbatar musu da cewa gwamnati za ta dawo da zaman lafiya tare da mayar da su gidajensu cikin aminci. Ya ce a wasu wurare ma har mata na fitowa domin kare iyalansu.

Gwamnan ya koka da cewa: "Wannan shi ne karo na farko da 'yan jihar Bauchi ke  gudun hijira. Jarrabawa ce, amma za a iya shawo kanta. Da yardar Allah za mu kawar da miyagun mutane mu dawo da zaman lafiya," in ji shi.

Gwamna Bala Mohammed ya yaba wa Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, da mutanen Kashere bisa haɗin kai da goyon baya. "Sun karɓi mutanenmu ba a matsayin ‘yan gudun hijira ba, sai dai a matsayin ‘yan uwa. Sun basu mafaka da abinci tun kafin zuwanmu. Wannan na nuna mu al’umma ɗaya ce," in ji shi.

Ya kuma tabbatar da ɗaukar matakin gaggawa ta hanyar samar da kayan abinci da agajin gaggawa tare da tallafin Naira miliyan 50 domin rage raɗaɗin halin da suka shiga.

"Jukunawa, Fulani da Jarawa duk daya muke. Na zo ne domin jajanta muku kuma domin ƙara hada kai domin shawo kan wannan matsalar," ya tabbatar.

Tun da farko, Kwamishinan ‘Yansanda na Jihar, CP Sani-Omolori Aliyu, ya sake jaddada ƙudirin rundunar na dawo da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa.

Shugaban ƙaramar hukumar Akko ta Jihar Gombe, Hon. Mohammed Danladi Adamu, ya ce ana ɗaukar matakai domin tallafa wa waɗanda suka rasa matsugunansu.

Ya ce bayan nan akwai kuma wasu 'yan gudun jiran a gundumomin Tukulma da Tarma a Akko waɗanda su ma ana kan tantance adadinsu, yayin da tallafin kuɗi da kayan abinci suka fara isa domin taimaka wa wadanda abin ya shafa.

Ya jajanta wa gwamnati da al’ummar Jihar Bauchi tare da bayyana kwarin gwiwar cewa Gwamna Bala Mohammed zai ɗauki matakan da suka dace domin dawo da tsaro a yankunan.

Daga nan Gwamna Bala Mohammed ya wuce Futuk domin jajanta wa Hakimin Futuk, Ahmad Sani Adamu, a Fadar Hakimin Futuk.

A yayin ziyarar, ya jajanta wa masarautar da al'ummar yankin kan wannan lamari mai muni, tare da sake jaddada kudirin gwamnatinsa na dawo da zaman lafiya da ƙarfafa tsaro a dukkan yankunan da abin ya shafa.





 

No comments