Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Nijeriya Ta Cancanci Samun ‘Yan Sandan Jihohi, Za A Zartar Da Zarar An Kammala Tanadin Doka – Minista

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya sake jaddada ƙudirin Gwamnatin Tarayya na kafa ‘yan sandan jihohi, yana mai...


Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya sake jaddada ƙudirin Gwamnatin Tarayya na kafa ‘yan sandan jihohi, yana mai cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙudiri aniyar ganin an aiwatar da shirin da zarar an samar da dokokin da suka dace.

Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin wata ziyarar girmamawa da Cibiyar Sadarwa kan Rikice-rikice (Centre for Crisis Communication, CCC) ƙarƙashin jagorancin shugaban ta, Manjo Janar Chris Olukolade (mai ritaya), ta kai masa a hedikwatar ma’aikatar da ke Abuja a ranar Alhamis.

Ya ce: “Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu yana son ya tabbatar da cewa mun samu ‘yan sandan jihohi da zarar hakan ya zama mai yiwuwa a wannan ƙasa. Lallai lokaci ya yi da za a aiwatar da hakan.”

Idris ya ƙara da cewa Shugaban Ƙasa ya riga ya roƙi Majalisar Dokoki da ta samar da dokokin da suka dace domin bai wa shirin damar tabbata.

Da yake magana kan muhimmancin sadarwa a zamanin dijital, Ministan ya ce: “A wannan zamani na fasahar dijital, rikice-rikice ba wai abubuwan da suka faru kaɗai ke haifar da su ba, har ma da yadda bayanai ke yaɗuwa cikin sauri. Saboda haka, sababbin fasahohin dijital suna da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da sadarwa daidai, cikin lokaci, kuma da tsari, musamman a lokutan da suke da muhimmanci ga ƙasa.”

Ya jaddada cewa dole ne ƙarfafa tsarin tsaron cikin gida ya tafi tare da inganta tsarin sadarwa na ƙasa, musamman ganin yadda yaɗuwar bayanai cikin sauri ke iya tasiri ga yanayin tsaro.

Idris ya yi maraba da shawarwarin cibiyar, ciki har da kafa Cibiyar Sadarwa kan Rikice-rikice ta Ƙasa da kuma Tsarin Auna Ingancin Sadarwa a Lokutan Rikici, yana mai cewa sun yi daidai da manufofin ma’aikatar.

Ya ba da tabbacin cewa ma’aikatar za ta yi nazari a kan rahoton taron ƙasa da aka gudanar a watan Nuwamba 2025 kan Sababbin Fasahohi da Sadarwa a Lokutan Rikici, domin duba yadda shawarwarin za su dace da sauye-sauyen da gwamnati ke aiwatarwa.

A nasa jawabin, Manjo-Janar Olukolade ya yaba wa Ministan bisa goyon bayan da ya bai wa shirin sauye-sauyen tsarin sadarwa a lokutan rikice-rikice a Nijeriya, yana cewa: “Matakin da ka ɗauka ya ƙara wa taron ƙima da nagarta, taron da ya haɗa masu magana da yawun hukumomi, ƙwararrun masana fasaha, jami’an tsaro, manazarta da ƙwararrun ‘yan jarida daga sassa daban-daban na ƙasar nan.”

Ya ce taron ya samar da shawarwari masu amfani da za su taimaka wajen zamanantar da tsarin sadarwar rikici ta hanyar ƙarfafa tsari, haɓaka ƙwarewa da kuma inganta haɗin gwiwa a tsakanin hukumomi.
 

No comments