Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ya kamata jam’iyyun Adawa Su Daina Kuka Da Ƙorafi Mara Tushe

  Wasu fitattun ’yan adawa, karkashin jagorancin jam’iyyun ADC da NNPP, sun taru a Abuja a yau inda suka yi furuci mara kan gado tare da zar...

 
Wasu fitattun ’yan adawa, karkashin jagorancin jam’iyyun ADC da NNPP, sun taru a Abuja a yau inda suka yi furuci mara kan gado tare da zarge-zarge na bogi kan Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da gwamnatin tarayya mai jagoranci a ƙarƙashin jam’iyyar APC.

Jam’iyyun adawa, musamman ADC, sun mai da fitar da kalaman siyasa marasa nauyi wata dabara ta jan hankalin kafafen yaɗa labarai, da nufin ruɗar jama’a.

Tare da haɗin gwiwar wasu ƙungiyoyin farar hula, ’yan adawar sun shafe lokaci suna yaɗa labaran ƙarya kan Majalisar Tarayya da gwamnatin Tinubu, suna ƙoƙarin matsa wa ’yan majalisa lamba, kasancewar su ne ke da ikon kundin tsarin mulki na yin dokoki domin inganta shugabanci a ƙasa.

Dangane da halin da ƙasa ke ciki, Majalisar Tarayya ta yi gyara ga Dokar Zaɓe wadda ta tanadi aika sakamakon zaɓe kai tsaye ta latroni tare da amfani da Form EC8A a matsayin madadi idan aka samu matsalar sadarwa. Ikirarin ’yan adawa cewa EC8A na buɗe ƙofa ga maguɗi ba shi da tushe, illa wata hayaniya ce ta waɗanda suka dage sai sunyi adawa.

Duk wani ɗan Najeriya mai hankali ya san cewa matsalolin sadarwa na faruwa. Dokar Zaɓe ta 2026 ba ta hana aika sakamako kai tsaye ba; kawai ta fayyace cewa idan aikawar ta gaza, sakamakon da aka rubuta a Form EC8A shi ne za a ɗauka a matsayin sahihi.

Haka nan, bai kamata a ruɗe jama’a kan rawar IReV ba. IReV ba cibiyar tara sakamako ba ce; dandali ne na ɗora sakamako domin jama’a su gani. Asalin takardar tabbatar da sakamakon zaɓe ita ce Form EC8.

A taron manema labaransu, jam’iyyun adawa sun kuma ƙi amincewa da amfani da zaɓen ƙato bayan ƙato (direct primaries) wajen fitar da ’yan takara. Abin mamaki ne ganin yadda suke kuka kan haɗa direct primaries da tsarin fahimtar juna (consensus), maimakon tsohon tsarin wakilai (delegates) da suka fi so, wanda ya yi ƙamari da cin hanci. Ya kamata su yaba wa Majalisar Tarayya da ta cire tsarin wakilai, ta mayar da ikon jam’iyya hannun mambobinta. Babu ɗan takara da ya kamata ya ji tsoron shigar mambobin jam’iyya kai tsaye. Wannan shi ne tsarin da ake amfani da shi a Amurka, inda aka aro tsarin mulkin demokraɗiyya.

Ikirarin cewa Majalisar Tarayya ta yi watsi da ra’ayin ’yan Najeriya ƙarya ne tsantsa. Tsawon shekaru biyu, a cewar Shugaban rinjayen Majalisar Dattawa, an saurari ra’ayoyin masu ruwa da tsaki, masana, da miliyoyin ’yan ƙasa, musamman game da barazanar matsalar fasaha da ka iya lalata dukkan zaɓe.

Wani jigon zargin ’yan adawa shi ne cewa Shugaba Tinubu na son mayar da Najeriya ƙasar jam’iyya ɗaya. Wannan magana ba ta da tushe. Najeriya ƙasa ce mai dimokiraɗiyya ta jam’iyyu da dama, sama da goma sha biyu, har da ADC da NNPP. Matsalar ’yan adawa ita ce rashin tsari da shirye-shirye, sannan su dinga ɗora laifi kan wasu. Shugaba Tinubu dan dimokiraɗiyya ne ƙwarai; shi ne jagoran adawa da ya taka rawa wajen kayar da PDP a 2015.

Sabanin yaɗa labaran ƙarya da nufin tayar da hankalin jama’a, sabuwar Dokar Zaɓe da Shugaba Tinubu ya sanya hannu a kai ta fi wadda aka soke inganci, domin ta rufe guraben da wasu ’yan adawa ke neman amfani da su wajen maguɗi.

A taƙaice, kuka da hayaniyar ’yan adawa ba komai ba ne face damuwa saboda an gyara ƙa’idojin almundahana don hana maguɗi irin su satar sakamako ta fasaha, abin da ake zargin sun saba da shi.

Maimakon wannan kuka da hayaniya marasa amfani, shugabannin ADC da NNPP su yi nazarin kansu tare da gyara matsalolinsu na cikin gida.

 

No comments