Mai Shari’a Justice Belgore, wanda ke sauraron ƙarar da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El‑Rufai ya shigar na tauye masa haƙƙinsa ya sanar da c...
Mai Shari’a Justice Belgore, wanda ke sauraron ƙarar da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El‑Rufai ya shigar na tauye masa haƙƙinsa ya sanar da cewa zai tafi hutu, lamarin da ya sa ya mayar da ƙundin shari’ar ga babban alƙalin babban birnin tarayya domin a sake ba wani alƙali daban ya ci gaba da sauraron ƙarar.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar da mai ba da shawara kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, ya fitar.
Tun a ranar Laraba 25 ga Fabrairu ne kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa yau, 27 ga watan Fabrairu domin sauraron ƙarar wanda ke neman kotu ta tilasta kare masa haƙƙoƙinsa da yake zargin an tauye.
Shari’ar na neman a ɗauki mataki kan hukumomin tsaro da suka haɗa da ICPC da EFCC da DSS da kuma Babban Lauyan Tarayya, bisa zargin take masa haƙƙinsa.
An tsare El-Rufai ne tun bayan da ya kai kansa ofishin EFCC da kansa domin amsa gayyatar da aka yi masaa ranar Litinin 16 ga Fabrairu 2026, kafin daga bisani a daren 18 ga watan aka sauya masa wuri zuwa hannun ICPC.

No comments