Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

AHMADU BELLO STADIUM: Gwamna Uba Sani Ya Kafa Tarihi A Arewacin Nijeriya ‎

‎Jihar Kaduna na daf da buɗe sabon babi a tarihin bunƙasa tattalin arziki da samar da ayyukan yi, bayan da Gwamna Uba Sani ya rattaba hannu ...



‎Jihar Kaduna na daf da buɗe sabon babi a tarihin bunƙasa tattalin arziki da samar da ayyukan yi, bayan da Gwamna Uba Sani ya rattaba hannu kan Yarjejeniyar Fahimtar Juna (MoU) wadda ta tabbatar da sauya mallaka da miƙa Filin Wasan Ahmadu Bello daga Gwamnatin Tarayya zuwa Gwamnatin Jihar Kaduna.

‎An cimma wannan matsaya ne bayan amincewar Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu. Gwamna Uba Sani ya sanya hannu a madadin Jihar Kaduna, yayin da Shugaban Hukumar Wasanni ta Ƙasa, Alhaji Shehu Dikko, ya sanya hannu a madadin Gwamnatin Tarayya.

‎Shugabannin Hukumar Wasanni ta Ƙasa sun yaba wa gwamnatin Kaduna bisa namijin kokarin da take yi wajen bunkasa harkokin wasanni, suna mai bayyana cewa jihar ta zama abin koyi ga sauran jihohin ƙasar nan.

‎A nasa jawabin, Gwamna Uba Sani ya jaddada cewa matakin zai mayar da wasanni wata muhimmiyar hanya ta habaka tattalin arziki, rage zaman kashe wando, da samar da guraben ayyukan yi musamman ga matasa. Ya bayyana cewa wasanni ba wai nishadi kadai ba ne, illa wata babbar hanya ta jawo zuba jari, bunkasa yawon bude ido, da farfado da kanana da matsakaitan sana’o’i.

‎Filin Wasan Ahmadu Bello, wanda aka gina tun shekarar 1964, a halin yanzu yana fuskantar cikakken gyara da sabuntawa domin kai shi matakin ka’idojin FIFA. Haka kuma, ana kara yawan kujeru daga 16,000 zuwa 32,000 domin ya dace da karbar manyan gasa na kasa da kasa.

‎Masu sharhi kan al’amuran yau da kullum na ganin wannan nasara a matsayin wani babban ci gaba ga jihar, inda suka bayyana cewa wannan shi ne karo na farko da aka samu cikakkiyar nasarar dawo da mallakar irin wannan katafaren filin wasa daga hannun Gwamnatin Tarayya zuwa jiha.

‎Ana sa ran kammala aikin gyaran filin wasan zai bude sabbin damammaki a fannin wasanni, kasuwanci da yawon bude ido, wanda hakan zai taimaka matuka wajen rage rashin aikin yi da kuma inganta rayuwar al’ummar Jihar Kaduna baki daya.

No comments