Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da cewa za a gudanar da aikin Tsabtace Muhalli na wata-wata a faÉ—in jihar a ranar Asabar, 28 ga watan Fabrai...
Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da cewa za a gudanar da aikin Tsabtace Muhalli na wata-wata a faɗin jihar a ranar Asabar, 28 ga watan Fabrairu, 2026, daga ƙarfe 7:00 na safe zuwa 10:00 na safe.
Kwamishinan YaÉ—a Labarai, Malam Ahmed Maiyaki, ya bayyana hakan a wata sanarwar manema labarai inda yace Gwamnatin ta sake jaddada Æ™udirin ta na tabbatar da dorewar muhalli, inganta lafiyar al’umma, da kuma kiyaye tsafta a dukkan sassan jihar.
Maiyaki ya Æ™ara da cewa dukkan kasuwanni, makarantu, wuraren aiki, tashoshin mota da sauran wuraren taruwar jama’a za su kasance a rufe har zuwa Æ™arfe 10:00 na safe domin bai wa mazauna damar fita su tsaftace muhallansu da unguwanninsu.
Shi ma Kwamishinan Muhalli, Abubakar Buba, ya jaddada muhimmancin wannan aiki na wata-wata, yana mai cewa yana daga cikin manyan matakan kariya da gwamnati ke É—auka domin inganta lafiyar jama’a.
Ya ce, “Aikin tsaftace muhalli na wata-wata ba kawai wani al’amari ne na yau da kullum ba; nauyi ne na haÉ—in gwiwa da ke da nufin kare lafiyar al’umma, hana É“ullar cututtuka, da tabbatar da tsafta da tsaro a Jihar Kaduna.”
Kwamishinan ya yi kira ga shugabannin al’umma, Æ™ungiyoyin ‘yan kasuwa, Æ™ungiyoyin direbobi da sauran mazauna da su tabbatar da cikakken bin wannan umarni a yankunansu, yana mai gargadin cewa duk wanda ya saÉ“a zai fuskanci hukunci daidai da dokokin muhalli da ke aiki.
Akan hakan gwamnatin Jihar Kaduna ta buÆ™aci al’umma da su É—auki wannan aiki da muhimmanci, tana mai jaddada cewa tsaftar muhalli nauyi ne na kowa da kowa tsakanin gwamnati da jama’a.

No comments