Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Dakta Malam Uba Sani, CON, ya karɓi baƙuncin mambobin Majalisar Limamai da Malamai daga sassa daban-daban na ji...
Taron wanda ya gudana a ranar Lahadi, 22 ga watan Fabrairu, 2026, ya haɗa manyan malamai da suka yaba da ƙoƙarin gwamnatin jihar wajen inganta zaman lafiya da haɗin kai, bunƙasa ci gaban al’umma a matakin ƙasa, da kuma ƙarfafa zaman jituwa tsakanin mabambantan addinai a faɗin jihar.
A jawaban da suka gabatar, malaman sun jaddada muhimmancin haɗin gwiwa, kyawawan halaye da addu’o’i wajen tabbatar da dorewar zaman lafiya, musamman a wannan wata mai alfarma na Ramadan. Sun kuma buƙaci a ci gaba da kyakkyawar alaƙa tsakanin shugabannin addini da gwamnati domin tinkarar ƙalubalen zamantakewa da ƙarfafa haɗin kan al’umma.
Da yake nasa jawabin, Sanata Dakta Malam Uba Sani, CON ya bayyana matuƙar godiyarsa ga Majalisar bisa halartar taron da kuma addu’o’in fatan alheri da suka yi domin dorewar zaman lafiya, ƙarfafa tsaro, da ci gaban gwamnatinsa.
Ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa na tafiyar da mulki cikin adalci, haɗin kai da manufofin da za su ƙara bunƙasa ci gaban Jihar Kaduna baki ɗaya.





No comments