Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Yaɗa Labaran Ƙarya Yana Haifar Da Babbar Barazana Ga Haɗin Kan Kasa, Inji Minista Idris

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi gargaɗin cewa yaɗa labaran ƙarya yana haifar da babbar barazana ga ɗabi’...


Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi gargaɗin cewa yaɗa labaran ƙarya yana haifar da babbar barazana ga ɗabi’a da haɗin kan ƙasa, inda ya yi kira ga matasan Nijeriya da su riƙa tabbatar da sahihancin duk wani labari kafin su yaɗa shi.

Ministan ya bayyana hakan ne yayin Laccar Ramadana ta Haɗin Gwiwa karo na 20 wadda Hukumar Talbijin ta Nijeriya (NTA), Hukumar Rediyon Tarayyar Nijeriya (FRCN) da gidan rediyon Muryar Nijeriya (VON) suka shirya a Kaduna.

Ya yi gargaɗin cewa amfani da kafafen sadarwa ta hanyar da ba ta dace ba yana iya ƙara rarrabuwar kawuna da raunana haɗin kan ƙasa.

A cewar sa, duk da cewa fasahar zamani ta kawo damammaki masu yawa, tana kuma zuwa da ƙalubalen ɗabi’a da ke buƙatar ladabi da ɗaukar alhaki.

Idris ya ce tantance sahihancin labari ya zama wajibi na ɗan ƙasa da kuma nauyin ɗabi’a a wannan zamani, yana mai cewa, “Sanin yadda kafofin watsa labarai suke aiki shi ne rigakafin yaɗuwar labaran ƙarya.”

Ministan ya buƙaci matasa da su yi amfani da kafafen dijital wajen neman ilimi, ƙirƙire-ƙirƙire da bunƙasa ƙasa, maimakon haifar da rarrabuwa.

Ya ƙara da cewa: “Ku tantance kafin ku yaɗa. Ku dakata. Ku binciki tushe,” yana mai jaddada cewa wajibi ne a yi amfani da fasahar zamani wajen ƙarfafa haɗin kai da cigaba.

Ya jaddada cewa yawan matasan Nijeriya na daga cikin manyan ƙarfin ta, amma makomar ƙasa tana dogara da yadda ake jagorantar su da tallafa masu.

Ya ce: “Ƙasar da ta kasa kula da matasan ta ba ta da makoma. Muna saka hannun jari a tsarin da zai mayar da fasahar dijital matattakalar samun damarmaki.”

Ministan ya bayyana cewa gwamnati tana aiwatar da shirye-shiryen tallafa wa matasa da dama a ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ciki har da shirin 3MTT, Lamunin Ilimi na Nijeriya (NELFUND), da kuma kafa cibiyar farko a Afrika ta koyar da ilimin kafofin watsa labarai.

Haka kuma, Ministan ya ambaci amincewar da UNESCO ta bai wa Nijeriya ta karɓar baƙuncin cibiyar farko a Afrika ta Ilimin Kafofin Watsa Labarai (IMILI), yana mai cewa wannan wani muhimmin mataki ne wanda zai taimaka wajen horar da jama’a kan tunani mai zurfi domin guje wa ruɗin labarai.

Ya nanata cewa kare ɗabi'a da sararin labarai ba aikin gwamnati kaɗai ba ne, yana kira ga iyaye, malamai, shugabannin addini, ‘yan jarida da matasa da su haɗa kai wajen gina al’umma mai fasaha da ɗabi’a tagari.

Laccar ta bana ta samu halartar gwamnonin jihohi da manyan jami’an gwamnati da sarakunan gargajiya da shugabannin kafafen yaɗa labarai daga sassa daban-daban na ƙasar nan.




No comments